Gwamnatin Najeriya ta ayyana mawallafin jaridar DESERT HERALD Tukur Mamu a jerin mutanen da ta ke tuhuma da daukar nauyin ta'addanci a Najeriya.
Tsohon Shugaban Mulkin Soja a Najeriya, Janar Abdussalam Abubakar yayi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa sojojin Najeriya 17 a jihar Delta dake Kudancin kasar.
A yau ne dai kungiyar NASU reshen jamiar legas tabi sahun sauran jami'oin Najeriya wajen shiga yajin aikin neman gwamnatin tarayya ta biya su albashin watanni hudu da suke bin gwamnati.
Mataimakiyar sakatarin al’adu da ilimi a ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka, Lee Satterfield, ta bayyana haka ne a jami’ar Legas a ranar Laraba inda ta bayyana manufofin kasashen waje kan sabbin shirye-shiryen.
Majalisar Dattawan Najeriya ta zartar da kudirin Dokar Rancen Dalibai da damar zurfafa karatu zuwa ta 2024 bayan yi masa kwaskwarima.
Wata gobara data tashi da a yau Laraba, a shagunan dake bangarorin nnamdi azikiwe da dacemo na kasuwar idumota ta jihar Legas, ta lalata dukiya ta miliyoyin nairori.
Al’ummomin dake zaune a yankin shiroro ta jihar Nejan Najeriya sun tabbatar da cewa rundunar sojin saman kasar ta kai wani hari ta sama da ya yi sanadiyyar tarwatsa garin Palale dake zaman matattara ta ‘yan ta’adda a yankin.
Mai Shari'a Binta Nyako ta Babbar Kotun Abuja, ta hana bada belin jagoran haramtacciyar kungiyar 'yan awaren Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu.
Dakarun Rundunar Zaratan Sojoji ta 3 da aka girke a yankin Maraban Maigora sun kubutar da mata 10 da yara 6 da 'yan bindiga suka yi garkuwa dasu tun a ranar 3 ga watan Fabrairun daya gabata.
Shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu ya amince da nadin sabon shugaban hukumar Almajirai da ilimin yara wadanda ba sa zuwa makaranta.
Hukumar kididdiga ta Najeriya NBS ta ce daga watan jiya na Febrairu, tashin farashin kayan masarufi a kasar ya kai 31.70%.
Al’umar garin Kajuru Station sun tabattar wa Muryar Amurka dawowan mutane uku cikin 87 da ‘yan bindiga suka sace a ranar Lahadin da ta gabata.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.