Shelkwatar Tsaron Najeriya dake Abuja ta ayyana neman daya daga cikin shugabannin haramtacciyar kungiyar 'yan awaren Biafra, Simon Ekpa, ruwa a jallo.
Dan Majalisar Dokoki ta jihar Sakkwato mai wakiltar mazabar Gada ta gabas Honorabul Haruna Dauda ya ce an ceto yaran ne bisa ga kokarin mai baiwa shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu da hadin guiwar gwamnatin jihar Sokoto.
Rundunar Sojin Najeriya tace dakarunta ba zasu bar yankin Naija Delta har sai an kama wadanda suka yiwa dakarunta 17 kisan gilla.
Dan wasan Najeriya Cyriel Dessers ne ya ci kwallon farko da bugun fenariti a minti na 38. A minti na 84 ne kuma Ademola Lookman ya zura tasa kwallon.
Sakamakon damuwa da tabarbarewar matsalar tsaro a Najeriya, gwamnoni 16 sun bayyana goyon bayan kafa 'yan sandan jihohi.
Dalibai biyu ne suka mutu, wassu da dama suka sami raunuka a wani turmutsutsu a jami'ar jahar Nasarawa dake garin Keffi, a gurin neman tallafi.
A makon da ya gabata dan takarar Shugaban kasa a zaben 2023 karkashin babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar ya yi kira da a gudanar da binciken “gaggawa” kan zargin na Ningi.
Tun bayan da labarin ya fantsama, abokan sana’arta da masoyanta suka yi ta wallafa sakon nuna alhini da yi mata fatan alheri.
A wani babban mataki na rage kudaden da ake kashewa, Shugaba Bola Tinubu ya sanya dokar hana tafiye-tafiye na tsawon watanni uku zuwa kasashen waje da ake amfani da kudaden gwamnati ga duk Ministoci, Shugabannin hukumomin gwamnati, da sauran jami’ai.
Kimanin mutane 21 ne ‘yan bindiga su ka hallaka da yammacin ranar Alhamis a jihar Nejan Najeriya.
Gwamnatin Najeriya ta ayyana mawallafin jaridar DESERT HERALD Tukur Mamu a jerin mutanen da ta ke tuhuma da daukar nauyin ta'addanci a Najeriya.
Tsohon Shugaban Mulkin Soja a Najeriya, Janar Abdussalam Abubakar yayi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa sojojin Najeriya 17 a jihar Delta dake Kudancin kasar.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.