Murja ta shigar da wannan kara ne karkashin jagorancin lauyoyinta wanda Barista Aliyu Usman Hajji ke jagoranta.
lauyoyin Murja dai sun ce hanyar da aka bi aka shigar da karar yana dauke da kura-kurai.
Wannan ne yasa lauyoyin ‘yar Tiktok din suka shigar da kara, a cewar su hukumar Hisbah ba ta da ikon mika mai laifi gaban kotu, wanda a kundin tsarin hukumar kamata ya yi da suka kamata su mika ta ga rundunar ‘yan sanda, domin gudanar da bincike tare da mika ta ga kotu ,wanda sabanin hakan ce ta faru.
Sannan sun sanya sunan kwamishinan ‘yan sanda a takardar karar, wanda ba akan haka aka shigar da kara ba - shima laifi ne, haka zalika ta hanyar da aka fara sauraron karar a kotun shari’ar Musulunci shima ba daidai aka yi ba, a cewar lauyan Murja, Barista Aliyu Usman Hajji.
Wadannan da ma wasu dalilan ya sa lauyoyin Murja suka ga dacewar shigar da bangarori guda bakwai kara gaban babbar kotun jihar Kano, duk da cewar ana kan sauraron shari’ar da ke gaban kotu na Murjar.
Tun da farko dai an shigar da Murjar kara karkashin kotun Musulunci, wanda ake tuhumarta da laifukan, da suka hada da hada kai da wasu kungiyoyi wajen tsoratarwar tare da gurbata tarbiya, da bayyana harkar badala da sauransu ta kafafar sadarwa ta Tiktok, wadannan sune tuhumomin da ake yi mata a gaban kotun Musulunci.
Barista Aliyu ya kara da cewa, bayan da aka gurfanar da Murja ta kuma musanta laifinta, an daga shari’ar ne da nufin za’a tsaya a matsaya na ba da belin Murja, ana dawowa kawai sai alkalin ya ce ya fuskancin cewar bata da hankali kamata ya yi a duba lafiyar kwakwalwarta.
Sai dai alkalin kotun ya tura shari’ar har na tsawon kwanaki casa’in, wanda shima wannan ba’a bi kundin tsarin mulki ba, shima yana daga cikin dalilan da ya sa suka shigar da kara, wannan da ma wasu dalilan ne ya sa suka shigar da kara gaban kotu.
Dandalin Mu Tattauna