Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AFDB Zai Zuba Dala Milyan 134 Domin Bunkasa Noman Abinci A Najeriya


Akinwunmi Adeshina
Akinwunmi Adeshina

Bankin Raya Kasashen Nahiyar Afrika (AFDB) ya sha alwashin tallafawa bangaren noman Najeriya da jarin dala milyan 134 da nufin bunkasa noman kayan abinci.

WASHINGTON DC - Shugaban AFDB, Akinwunmi Adesina ne ya bayyana aniyar yayin ziyarar Cibiyar Nazarin Noman Tsandauri ta Jami'ar Bayero dake Kano.

Adesina ya kuma jaddada mahimmancin samawa manoma bayanai akan kari, musamman ma yanzu da ake fama da kalubalen sauyin yanayi.

Har ila yau, Adesina ya bayyana aniyar bankin ta bunkasa ci gaban fasaha a harkar noma, inda yace, "zamu hada kai da cibiyar nazarin noman tsandauri domin inganta ayyukanta a bangaren hasashen yanayi da tattara bayanai, ta haka zamu tallafawa manoma su gudanar da tsare-tsare yadda ya dace.

Haka kuma, Shugaban Bankin na AFDB ya jinjinawa kokarin Shugaban Jami'ar Bayero ta Kano, Farfesa Sagir Adamu-Abbas da daraktan Cibiyar Nazarin Noman Tsandauri, Jibrin Muhammad Jibrin saboda tallafin da suke baiwa manoma wajen yin amfani da fasaha a harkar noma a irin wannan lokaci da ake yaki da sauyin yanayi.

A martaninsa, Shugaban Cibiyar Nazarin Noman Tsandauri, Jibrin Muhammad Jibrin ya tabbatar da aniyar cibiyar ta maida hankali kan bincike da koyar da dabarun samun ci gaba ta hanyar maida hankali kan noman tsandauri.

Zuba dimbin jarin da AFDB yayi gami da mahimmancin daya baiwa amfani da fasaha a harkar noma da yin amfani da tsiran dake iya jurewa yanayi na nuni da samun ci gaba wajen samun bunkasar noma, ta haka za'a samu wadatuwar kayan abinci da bunkasar tattalin arziki yankin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG