Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Ma’aikatan Wutar Lantarki Ta Kori Ma’aikata Da Rufe Ofishinsu A Kaduna


Ofishin wutar lantarkin jihar Kaduna KAEDCO
Ofishin wutar lantarkin jihar Kaduna KAEDCO

Mambobin kungiyar NUEE sun kasa sun tsare a gaban babban ofishin hukumar raba wutar lantarki ta jihar Kaduna.

KADUNA, NIGERIA - Ma’aikatan na ganin akwai sakaci da rashin kula da biyan hakkokinsu.

Ma’aikatan gidan wutar lantarki na Kaduna da aka kora daga aiki
Ma’aikatan gidan wutar lantarki na Kaduna da aka kora daga aiki

Hakan yasa da sanyin safiyar yau Talata kungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta NUEE reshen jihar Kaduna ta kori ma’aikata tare da garkame babban ofishin hukumar gudanarwar samar da wutar lantarki ta jihar KAEDCO sakamakon rashin biyan ma’aikatan hakkokinsu.

Kungiyar NUEE dai tace ta dauki wannan matakin ne sakamakon wasu bukatun ma’aikata da ta ce ta dade tana bin hukumar KAEDCO ta biya musu amma abun yaci tura, inda a yanzu turi ta kai bango.

Ma’aikatan gidan wutar Lantarki na Kaduna a wajen ofishin bayan an kore su daga aiki
Ma’aikatan gidan wutar Lantarki na Kaduna a wajen ofishin bayan an kore su daga aiki

Da yake maida martini kan matakin na NUEE, Shugaban hulda da jama’a na KAEDCO, Abdulaziz Abdullahi yace akwai alkawarin zama da sukayi da kungiyar a Laraba don gabatar musu da matakan da suke dauka don samar da maslaha amma duk da haka suka dauki wannan mataki.

A watan daya gabata ne dai Ministan Lantarki na Najeriya ya sanar da cewa akwai yiyuwar cire tallafin wutar lantarki sakamakon yawan bashin da ake bin kamfanonin samar da wutar lantarki na kasar da ya haura Naira tiriliyon uku.

A halin da ake ciki a Najeriya na matsala da kuma karancin wutar lanatarki, kama daga jihohi harma da birnin tarayyar kasar, inda ake shafe sa’o’i a wasu lokutan ma kwanaki babu wutar lantarki.

Saurari cikakken rahoto daga Hauwa Umar:

Kungiyar Ma’aikatan Wutar Lantarki NUEE Reshen Jihar Kaduna Ta Kori Ma’aikata Da Rufe Ofishinsu .mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG