Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ga Watan Azumin Ramadan A Najeriya


Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar III
Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar III

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar III ya sanar da ganin watan azumin Ramadan a Najeriya.

Sarkin musulmi ya ce sun sami labarin tabbacin ganin watan Ramadan daga shugabanni da kungiyoyi na addinin musulunci, kuma sun amince.

Ya yi kira ga dukkan Musulman Najeriya da su tashi da azumin watan Ramadan gobe Litinin.

Haka kuma, ya yi kira ga al’ummar musulmi a fadin Najeriya da su dage da addu’o’i don fitar da kasar daga cikin halin kunci da aka samu kai ciki.

Tun farko dai Jami’an Saudiyya sun sanar da ganin jaririn watan Ramadan. Ba da jimawa ba, kasashen Larabawa da dama na yankin Gulf, da Iraki da Siriya, sun bi sanarwar don tabbatar da cewa su ma za su fara azumi ranar Litinin.

Shugabannin sun kuma yi ta musayar sakonnin taya murna cewa an shiga watan Ramadan mai alfarma.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG