Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Fara Duban Watan Ramadan Daga Yau Lahadi - Sarkin Musulmi


Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar III
Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar III

A Najeriya, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, kuma Shugaban Majalisar Koli ta Addinin Musulunci, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar (III), ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su fara duban watan azumin Ramadan daga yau Lahadi.

Sarkin Musulmi Abubakar, ya yi wannan kiran ne a wata takardar bayani mai dauke da sa hannun Farfesa Sambo Junaidu, Ciyaman din Kwamitin Bayar Da Shawarwari kan harkokin Addini, na Majalisar Masarautar, wadda aka bai wa manema labarai.

Da wannan, ana bukatar Musulmi su fara duban sabon watan Ramadan, tare da bayar da rahoto da zarar an gani, ga Hakimi ko Sarki mafi kusa, don tura bayanin ma Mai Alfarma Sarkin Musulmi.

Ramadan, wanda shi ne wata na tara a kalandar Musulunci, lokaci ne na azumi, wanda daya ne daga cikin shika shikai biyar na addinin Musulunci.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG