Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kuskuren Bayanan Sirri Na Kawo Cikas A Yakin Da Ake Yi Da Masu Garkuwa Da Mutane – Janar Musa


Babban Hafsan Tsaron Najeriya Janar Christopher Gabwin Musa
Babban Hafsan Tsaron Najeriya Janar Christopher Gabwin Musa

Babban hafsan tsaron Najeriya Janar Chris Musa ya ce masu ba da bayannan sirri ga sojojin ke kawo cikas ga yaki da kungiyoyin masu garkuwa da mutane da ke ci gaba da sace dalibai da mazauna arewacin kasar. 

Babban hafsan tsaron Najeriya Janar Chris Musa ya ce masu ba da bayannan sirri ga sojojin ke kawo cikas ga yaki da kungiyoyin masu garkuwa da mutane da ke ci gaba da sace dalibai da mazauna arewacin kasar.

Janar Musa ya bayyana hakan ne a ranar Litinin.

A ranar Lahadin da ta gabata ne rundunar sojin ta sanar da kubutar da dalibai 137 da wasu ‘yan bindiga suka sace a farkon watan nan a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin kasar. ‘Yan makarantar sun isa Kaduna ne a ranar Litinin.

Daliban Makaratar Kurigan Da Aka Kubutar
Daliban Makaratar Kurigan Da Aka Kubutar

Musa ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa sojoji a matse suke kuma galibi suna dogara ne ga masu ba da bayannan sirri don bin gungun masu dauke da makamai, wadanda aka fi sani da ‘yan bindiga a cikin gida, ba tare da samun nasara ba.

“Su masu ba da bayannan sirri su kan sa sojojin su je wani wuri na daban, sai sun isa wurin sai su tarar ba komai,” in ji Musa.

Musa ya ce babu wata arangama da ‘yan bindigar a lokacin da aka ceto daliban na Kaduna. Sai dai ba zai bayyana yadda aka kubutar da daliban ba ko an cafke wani daga cikin ‘yan bindigar.

Yan bindiga
Yan bindiga

An yi garkuwa da mutane akalla 68 a cikin kwatan farko na shekarar 2024 akasari a arewacin Najeriya, a cewar wani kamfanin tuntuba na kasada, SBM Intelligence.

Musa ya ce da zarar ‘yan bindiga sun shiga dazuzzukan Najeriya, ya kan yi wuya a bi su saboda da sauri-sauri ’yan bindigar ke tafiya cikin dajin.

“Da zarar sun shiga ciki, fitar da su ke da wuya, da wuya jiragen sama ke iya ganinsu,” in ji shi, ya kara da cewa iyakar arewacin kasar da ba shi da kawanya, ya kara dagula lamarin.

Satar mutanen dai ta sa wasu gwamnatocin jihohi daukar abin da suka kira masu gadin al’umma.

“Yanzu gwamnatocin jihohi da kansu za su debo mutanen da ba su da horo su tura su kuma muna hana su yin hakan,” in ji shi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG