WASHINGTON, D. C. - Sanusi Dawakin Tofa, Darakta Janar na yada labarai ga jama’a ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Lahadi a jihar Kano.
Ya ce gidauniyar Dangote ta kuma tallafa wa jihar da buhunan shinkafa 120,000 10kg.
“Bayan wannan tallafin, gwamnatin jihar za ta bayar da tireloli 145 na hatsi iri-iri domin rabawa ga kananan hukumomi 44 da unguwanni 484,” inji shi.
Mr. Tofa ya ce sun yi hakan ne tare da hadin gwiwar kananan hukumomin jihar.
Ya ce gwamnatin jihar ta kuma fara gudanar da bincike kan shirin ciyar da mutane a cikin watan Ramadan da ake yi a fadin jihar.
Tofa ya ce Gwamna Abba Yusuf ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda shirin ke gudana a lokacin da ya kai ziyarar ba-zata zuwa wasu zababbun cibiyoyin ciyar da jama’a na Ramadan da ke cikin birnin na Kano.
“Yusuf ya nuna rashin jin dadinsa da abin da ya gani a cibiyoyin, inda ya yi tambayoyi da dama wadanda ba su da amsoshi daga masu gudanar da shirin.
"Gwamnan ya ce nan da sa'o'i 24 masu zuwa, gwamnati za ta sake tsara kwamitin ciyar da abinci da ke gudanar da aikin," in ji shi.
Mr. Tofa ya ce gwamnatin jihar ta kebe cibiyoyi 80 na ciyar da abinci a kananan hukumomi takwas, kuma manufar ita ce ciyar da mutane 1,000 a kullum a kowace cibiya.
"Yusuf ya kasance a cibiyoyin ciyar da abinci kuma ya ga abin da ke faruwa kuma maimakon saduwa da ainihin mutane 1,000 da aka yi niyya, an ciyar da 450 ne kawai a cibiyoyin da ya ziyarta," in ji shi.
Mr. Tofa ya ce saboda halin da ake ciki a cibiyoyin, gwamnan ya ba da umarnin sake tsara kwamitin da zai tafiyar da aikin sosai.
Ya kuma ba da umarnin gudanar da bincike kan dukkan ayyukan da nufin hukunta masu laifi.
Dandalin Mu Tattauna