Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Yi Nasarar Kubutar Da Mutane 16 Da Aka Yi Garkuwa Dasu A Katsina Bayan Shafe Kwanaki 46 A Hannun 'Yan Bindiga


Sojoji Najeriya kusa da Maiduguri, Mayu 14, 2015.
Sojoji Najeriya kusa da Maiduguri, Mayu 14, 2015.

Dakarun Rundunar Zaratan Sojoji ta 3 da aka girke a yankin Maraban Maigora sun kubutar da mata 10 da yara 6 da 'yan bindiga suka yi garkuwa dasu tun a ranar 3 ga watan Fabrairun daya gabata.

WASHINGTON DC - Wata majiya daga rundunar sojin ta bayyana cewar an kubutar da mutanen ne yayin wani aikin sintiri a kauyen rimi bayan da suka shafe kwanaki 46 a hannun 'yan bindiga.

Wadanda da aka kubutar din na daga cikin mata 54 da aka sace akan hanyar Gamji zuwa Dandume a farkon watan Fabrairun daya gabata.

Mata da yara da aka kubutar daga hannun 'yan bindiga
Mata da yara da aka kubutar daga hannun 'yan bindiga

Biyo bayan kubutar dasu da aka yi a jiya litinin, an mika matan da yaran hannun Shugaban Karamar Hukumar Sabuwa, wanda shi kuma ya sadasu da danginsu.

Da yake tabbatar da afkuwar lamarin, Gwamna Dikko Radda cikin wata sanarwa da babban sakatarensa akan harkokin yada labarai Ibrahim Kaula Muhammad ya fitar a jiya Litinin, ya yabawa dakarun saboda jarumta da daukar matakin daya dace da suka yi.

Gwamnan wanda ya jinjina girman lamarin, ya baiwa al'umma tabbacin kudirin gwamnatinsa na kawo karshen matsalar 'yan bindiga a fadin jihar Katsina.

Mata da yara da aka kubutar daga hannun 'yan bindiga
Mata da yara da aka kubutar daga hannun 'yan bindiga

A cewar sanarwar, aikin kubutar da wadannan mata da yara shaida ce game da kwarin zuciya da jajircewar dakarun tsaronmu. Mun kudirin aniyar sama musu dukkanin kayan aikin da goyon bayan da suke bukata domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron al'umma.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG