Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tashin Farashin Kayan Masarufi A Najeriya Ya Haura Zuwa 31.70% - NBS


Kayayyakin Masarufi  
Kayayyakin Masarufi  

Hukumar kididdiga ta Najeriya NBS ta ce daga watan jiya na Febrairu, tashin farashin kayan masarufi a kasar ya kai 31.70%.

Wannan ya nuna kari daga alkaluman baya na kashi 29.90%.
Idan an kwatanta da bara, daidai Febrairu an samu karin kashi 9.79%.
A hirar shi da Muryar Amurka, wani talaka Muhammad Salisu ya nuna damuwa kan kuncin da talakawa ke ciki.

Shinkafa da sarafata
Shinkafa da sarafata

Bayanan kungiyar ta NBS sun nuna sashin kudu maso yammacin Najeriya ya fi tsadar abinci inda arewa maso yamma ya fi samun rangwame.


Mai taimakawa Shugaba Tinubu kan labaru Abdul'aziz Abdul'aziz ya ce don magance kunci ne ya sa Shugaba Tinubu ganawa da shugabannin kasashe masu arziki don zuba jari a Najeriya kamar yadda ya faru kwanan nan a Daular Larabawa.

Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmad Tinubu da Sarkin Qatar, Mai Martaba Sheikh Tamim Bin Hamad Al-Thani
Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmad Tinubu da Sarkin Qatar, Mai Martaba Sheikh Tamim Bin Hamad Al-Thani

Tun cire tallafin man fetur da Shugaba Tinubu ya yi a ranar 29 ga Mayun bara a ke samun karin tsadar rayuwa a Najeriya.


Sai dai a bayaninsa, masanin tattalin arziki kuma shugaban 'yan arewa mazauna kudu Ambasada Musa Sa'idu ya ce kalubalen ya wuce na cire tallafin.


A Najeriya dai yanzu ga zafin rana ga na aljihu sai jiran tsammanin alkawarin sauki.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG