Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisa Ta Bayyana Dalilin Dakatar Da Sanata Ningi


Taron yan majalisa da sanatoci
Taron yan majalisa da sanatoci

Sanata Abdul Ningi dai dan Jam'iyyar PDP ne kuma shi ne Shugaban Kwamitin kula da Yawan Jama'a wato National Population Committee sannan kuma Shugaban Kungiyar Sanatocin Arewa a Majalisar Dattawan.

Bayan dakatar da Sanata Abdul Ningi kan zargin da ya yi cewa Majalisa ta yi cushe har na kudi Naira Tiriliyan 3 da 'yan kai a kasafin kudin wannan shekara, wasu sanatocin daga shiyyar Arewa sun jaddada wa Muryar Amurka cewa dakatar da Abdul Ningi ta na kan hanya amma Sanata Agom Jarigbe ya ce zargin da Ningi ya yi gaskiya ce.

Abdul Ningi
Abdul Ningi

Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ne ya sanar da dakatar da Sanata Abdul Ningi mai wakiltar Bauchi ta tsakiya har na tsawon watanni uku kan zargin da ya yi cewa Majalisa ta yi cushen Naira tiriliyan 3.7 a kasafin Kudin wannan shekara, sannan ya ce ana amfani da kasafin kudi guda biyu ne a yanzu haka.

Sanata Abdul Ningi dai dan Jam'iyyar PDP ne kuma shi ne Shugaban Kwamitin kula da Yawan Jama'a wato National Population Committee sannan kuma Shugaban Kungiyar Sanatocin Arewa a Majalisar Dattawan.

Godswill Akpabio
Godswill Akpabio

A zaman Majalisar Dattawan na jiya Talata dai, wannan magana ta jawo hayaniya a zauren majalisar inda aka tada jijiyar wuya, har Sanata Adeola Olamilekan, wanda shi ne Shugaban Kwamitin kula da Kasafin Kudi a Majalisar, ya karanta fassarar hirar da Abdul Ninigi ya yi da gidan Radiyon BBC inda ya yi zargin cushen, kuma ya bada shawarar a kafa wani kwamiti na wucin gadi da zai binciki zargin na Ningi.

To sai dai Sanata mai wakiltar Jihar Neja ta Gabas kuma Shugaban kwamitin kasafin kudi Mohammed Sani Musa ya musanta zargin cushen kudin inda ya ce a saninsa dai majalisa ta aiwatar da kasafin kudi na Tiriliyan 28, kuma kason da aka yi na manyan ayyuka bai kai yadda ake ta yayatawa ba.

Sani ya ce yana kira ga yan'uwansa na Majalisa da su rika sara suna duban bakin gatari, su rika sanin abin da zai fito a bakinsu domin duk abinda ya fito shi ne yan Najeriya za su amince da shi.

A lokacin da yan majalisan ke tafka zazzafar mahawara kan tsawon lokacin da ya kamata a dakatar da Abdul Ningi, Sanata Jimoh Ibrahim ya ce a dakatar da shi na tsawon shekara daya sannan ya ce a ja wa Sanata Suleiman Kawu Sumaila kunne kan yayata zargin a dandalin sada zumunta.

Amma Sanata Garba Maidoki daga Jihar Kebbi ya sake gyara kudurin cewa an dakatar da Abdul Ningi na wattani 3 kuma a bashi dama na neman ahuwa. Majalisar ta amince da wannan gyara da Maidoki ya yi.

Sanata Mohammed Ali Ndume
Sanata Mohammed Ali Ndume

Amma Sanata Mohammed Ali Ndume Babban mai tsawatarwa a bangaren masu rinjaye, yayi tsokaci yana cewa, suna fatan shi Ningi zai gane kuskuren sa ya rubuta wasika ta bada hakuri, kuma ya yi wa BBC Hausa bayani inda yayi magana cewa an samu kuskure, kuma yana bada hakuri. Ndume ya ce Sanatoci Arewa ba su ki shi ba, amma su dattawa ne. Ndume ya ce su sanatoci Arewa za su tsaya wa Arewa, babu yadda za a yi a cuci Arewa suna kallo. Ndume ya ce daga Majalisar Wakilai har na Dattawa, yan Arewa ne suka fi yawa. Saboda haka za su tsaya wa Arewa.

To saidai biri yayi kama da mutum, domin Sanata Jarigbe Agom Jarigbe da Jihar Kros Ribas ta Arewa ya ce wasu sanatoci sun samu Naira Miliyan 500 ko wanne daga cikin kasafin kudin na bana.

Jarigbe ya ce idan muna son shiga cikin wannan batu, dukkanmu muna da laifi, wasu sanatoci suna da wannan dabi'ar, ni ina da tabbacin cewa manyan sanatoci sun samu Naira miliyan 500 ko wannensu, in batun manya ne, ni ma babban Sanata ne, amma ba a ba ni ba.

Abin jira a gani shi ne tsawon lokacin da zai dauka kafin Abdul Ningi ya aiko da takardar neman ahuwa, ko da ya ke ya riga ya aiko da takardar murabus daga shugabancinsa na kungiyar Sanatocin Arewa.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:35 0:00

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG