Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Samu Tallafin Dala Biliyan 1.3 Don Karasa Hanyar Jirgin Kasa Daga Kano Zuwa Nijar


Wani Layin Dogo A Mexico
Wani Layin Dogo A Mexico

Najeriya ta samo tallafin dala biliyan 1.3 domin kammala aikin layin dogo da zai hada Kano, birni mafi girma a arewacin Najeriya zuwa Maradi dake makwabciyar kasar Nijar, in ji ma'aikatar sufuri a ranar Laraba.

WASHINGTON, D. C. - Ana sa ran layin dogon zai karfafa tattalin arziki da zamantakewar da ke tsakanin kasashen domin bunkasa huldar kasuwanci da al'adu tsakaninsu.

Sanarwar da ma'aikatar sufuri ta fitar ta ce, za a ba da tallafin ne daga wata gamayyar hadin gwiwa da kamfanin gine-ginen na kasar Sin (CCECC) ke jagoranta, wanda zai ba da kaso 85% na jimillar kudaden.

Gwamanatin Najeriya kuma za ta biya sauran kaso 15% tare da bankin fitar da shigar da kaya na Afirka da kuma bankin raya kasashen nahiyar Afirka.

Kakakin ma'aikatar sufuri Jamilu Ja'afaru ya ce "samun dalar Amurka biliyan 1.3 na nuni da wani gagarumin ci gaba wajen kammala wannan muhimman ababen more rayuwa."

A watan Yuli, kamfanin gine-gine mafi girma a kasar Portugal Mota-Engil ya rattaba hannu kan wata kwangilar Euro miliyan 840 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 919 don samarwa da kuma ba da kuɗin jigilar layin dogon.

Gwamnatin Najeriya ta yi kokarin sake gina arewacin kasar da ke fama da talauci, wanda wasu sassa na kasar suka yi barna tun shekaru goma da suka gabata a hannun masu kaifin kishin Islama.

Wannan aiki dai wani shiri ne na gina layin dogo a fadin Najeriya domin magance rashin wadatattun ababen more rayuwa da ke kawo cikas ga ci gaban tattalin arzikin kasar shekaru da dama

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG