Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Makon 'Yan Jaridu: ‘Yan Jarida A Najeriya Sun Bayyana Kalubalen Da Su Ke Fuskanta


Taron manema labarai a Jihar Nejan, Najeriya
Taron manema labarai a Jihar Nejan, Najeriya

A yayin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da kokawa kan tsananin tsadar rayuwa a kasar, suma ‘yan jaridun kasar sun ce suna cikin yanayi na tsaka mai wuya musamman yadda aikinsu na kokarin ankarar da gwamnati halin da ‘yan kasar ke ciki da kuma hanyoyin shawo kan matsalolin da suke fuskanta.

MINNA, NIGERIA - Ko baya ga matsalar tsadar rayuwa a yanzu, matsalar rashin tsaron da ya addabi sassan Najeriya na zama kalubale ga manema labaran kasar musamman idan aka yi la’akari da irin kiki-kaka da ake samu a tsakaninsu da hukumomin kasar wajan samun sahihan bayanai da ya kamata a baiwa al’umma da zai taimaka wajan kwantar da hankalinsu.

Taron manema labarai a Jihar Nejan, Najeriya
Taron manema labarai a Jihar Nejan, Najeriya

A wani babban taro na makon ‘yan jaridu da ya gudana a jihar Neja, an gabatar da jawabai tare da karawa manema labaran kwarin guiwa akan aikinsu na taimakon ‘yan kasa.

Sakataren Kungiyar ‘Yan Jaridu ta NUJ a jihar Neja, Kwamred Usman Chiji yace babban taron ya nuna bukatar kulawa ta musamman ga ‘yan jaridu na jihar da kuma kasa baki daya.

To amma neman hanyoyin shawo kan matsalolin da suka addabi Najeriya shine ya dauki hankalin wasu ‘yan jaridu da suka halarci taron.

Daga hagu, Babban Daraktan gidan rediyon Muryar Najeriya, Jibrin Baba Ndace a taron manema labarai a jihar Neja.
Daga hagu, Babban Daraktan gidan rediyon Muryar Najeriya, Jibrin Baba Ndace a taron manema labarai a jihar Neja.

Gwamnatin Najeriya dai ta ce tana kokarin shawo kan matsalolin da ‘yan kasar suke fuskata.

Ministan labaran Najeriya Muhammad Idris Malagi wanda babban daraktan gidan rediyon Muryar Najeriya, Jibrin Baba Ndache, ya wakilta a wannan taro ya nuna bukatar ganin ‘yan jaridun sun maida hankali wajen wayar da kan ‘yan kasa duk kuwa da kalubalen da suke fuskanta.

Da dama daga cikin ‘yan jaridu na samun kansu cikin hali na barazana daga bangarorin jama’a ko ma na gwamnati a kasar, a kokarinsu na yin aikinsu kamar yadda doka ta tanada.

Saurari cikakken rahoto daga Mustapha Nasiru Batsari:

Kalubalen Da ‘Yan Jarida Ke Fuskanta A Najeriya.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG