Wani ganau wanda ya zanta da jaridar Tribune ta Najeriya, yace matashin, wadda ba a bayyana sunansa ba, ya rasu ne kafin bugun karshe daya baiwa Najeriya damar kaiwa ga zagayen karshe na gasar cin kofin nahiyar Afrika.
Ya kara da cewar, “mun yi rashin dan Najeriya gudu ‘yan dakikoki kadan da suka gabata sa’ilin da muke murnar samun nasara akan Afrika ta Kudu a gidan kallonmu dake nan garin Numan”.
Da yake tabbatar da mutuwar, Shugaban Hukumar NYSC na jihar adamawa, Jingi Dennis, yace wani likita a babban asibitin garin Numan ne ya ayyana cewar dan bautar kasan ya rasu.
Ya kara da cewar, “na samu labarin mutuwar tasa a daren jiya, ina fatan samun cikakken bayani akan haka a yau.”
“A cewar abokan aikinsa da suka je kallon kwallon tare, marigayi dan bautar kasar ya bayyana masu cewar bai faye son kallon bugun daga kai sai me tsaron raga ba, daga nan sai ya dukar da kansa sa’annan ya fadi.”
“Wani likita a babban asibitin garin Numan ne ya tabbatar da mutuwarsa.”
Haka ma wani jigo a jam’iyyar APC a jihar Delta, Cairo Ojuogboh ya rigamu gidan gaskiya bayan ya yanke jiki ya fadi yana kallon wasan.
Marigayin ya taba zama mamba a Majalisar Wakilan Najeriya tsakanin (2003-2007).
Da yake martani akan lamarin, tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, yace mutuwar Ojuogboh wani babban rashi ne a gare shi.
A sakon daya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya rubuta cewar: “Nayi takaicin rashin aminina, Dr. Cairo Ojuogbo. Soyayyarsa ga kasarmu ba zata kwatantu ba.”
“Cairo wani alama ne na tsantsar kishin kasa; babu tantaba game da hidimarsa ga Najeriya, rasuwarsa wani rashi ne a gareni daya bar gurbi a zuciyata. A daidai lokacin da muke alhinin mutuwarsa, ya kamata mu duba yadda ya siffantu da tsananin so da kaunarsa ga Najeriya. Muna yi masa addu’ar samun rahama.”
Har ila yau, shima Mataimakin Ma'aji na Jami’ar Jihar Kwara, Malete, Alhaji Ayuba Abdullahi, ya rasu a daren ranar Larabar bayan da rahotanni suka ce ya kamu da cutar hawan jini a lokacin da yake kallon wasan na kusa da na karshe tsakanin Najeriya da Afrika ta Kudu a gasar AFCON da ke gudana.
An tabbatar da mutuwar Ayuba a cikin wata sanarwa da mahukuntan jami’ar suka fitar a safiyar yau Alhamis.
Majiyar ta bayyana cewa, marigayin ya je wata cibiyar wasanni da ke unguwar Sango a garin Ilorin domin kallon wasan, amma bayan karin lokaci ya bar wajen domin jin damuwa a jikinsa.
Mataimakin Ma'ajin ya kalli wasan na Najeriya da Afirka ta Kudu tun daga farko har zuwa karshen karin lokaci, har lokacin bugun fanareti sannan ya ci gaba.
Ya koka da cewa yana jin jiri, ya yanke shawarar komawa gida ya huta bai san jininsa ya haura ba.
Ya na komawa gida sai ya fadi, aka garzaya da shi wani asibiti mai zaman kansa da ke Sango inda suka ce a wuce da shi asibitin koyarwa na Jami’ar Ilorin amma kuma kafin akai ga duba shi ya rasu.
Wasan kusa dana karshen, wanda aka tashi kunnen doki ci 1-1 bayan karin lokaci, inda Super Eagles ta samu nasara a bugun daga kai sai mai tsaron raga, ya kasance mai cike da tashin hankali.
Dandalin Mu Tattauna