Bisa tsari irin na gwamnati, gwamnati ne ya kamata ta jajirce wajen tabbatar da cewa, talakan kasa ya samu duk wasu abubuwan more rayuwa da kuma walwala.
Sai dai a Najeriya tun daga lokacin da aka cire tallafin man fetur tsadar rayuwa ta ke kara ta’azzara. Haka kuma dimbin harajin da gwamnatin ke dorawa al’ummar kasar ya zamo tamkar talaka ne ke daukar nauyin gwamnatin.
A hirar shi da Muryar Amurka, ‘Mukhtar Muri dake kantin kwari a jihar kano ya bayyana cewa, ‘yan kasuwa na fukantar barazana kan harajin da a ke yawan karba a wajen su.
A nashi bayanin, mai sharhi kan tattalin arziki Abubakar Ali yace, "Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya na so ya yi amfani da salon samar da kudaden shiga kamar yadda ya yi a lokacin da ya ke Gwamnan jihar Legas, amma bai yi la’akari da halin da kasar, da kuma al’ummar kasar ke ciki a yanzu ba."
A jawabinsa game da yawan harajin, Ministan yada labaru Muhammad Idris ya ce, "gwamnati za ta duba tsarin biyan harajin domin al’ummar kasar su samu sauki."
Hukumar tattara kudaden shiga ta yi hasashen cewa, kudaden shiga zai karu da kashi 57 cikin dari a shekarar 2024 zuwa Naira tiriliyan 19.4 idan aka kwatanta da bara.
Saurari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna