KANO, NIGERIA - Mutane da dama gami da ‘yan unguwar su Murja Ibrahim Kunya ne suka kai korafe-korafen game da yadda Murja ke bata musu tarbiyar yara a unguwar tare da cewa gwamnati ta ki hukuntata.
Ko a watanni biyu da suka wuce hukumar ta Hisbah ta nemi wasu fitattun ‘yan TikTok su shida domin jan hankali tare da nuna musu illar irin kalaman su da yadda suke bata tarbiya.
A ranar Litini ne hukumar ta Hisbah ta samu damar cafke Murja inda kuma a ranar Talata aka gurfanar da ita a gaban hukuma.
Tuni dai kotu ta aike da Murja gidan gyaran hali har sai ranar 20 ga watan Fabarairun wannan wata inda kotu zata sake sauraron karar, amma kuma kotun ta ki bada belin jarumar Tiktok din.
An dai kama Murja ne tare da saurayinta wanda bayan tuhumarta da yi mata wa’azi da neman ta da shiri, tuni dai Murja ke gıdan gyara hali a halin yanzu.
Akan haka ne Muryar Amurka ta tuntubi hukumar ta Hisbah tun da farko inda suka bayyana irin matakan da suka dauka na nusar da ita a lokuta da dama amma babu sauyi inda har aka kai gabar da aka kai ta kotu.
Babban Mataimakiyar Kwamanda Hisbah Dr. Khadija Sagir Suleiman ta ce Murja bata fi karfin hukuma ba, amma asali ma a lokuta da dama bayan yi mata wa’azi sai ta koma gidan jiya.
Dr. Khadija ta ce yunkurin hukumar ta Hisbah domin magance matsalolin ‘yan TikTok ne da suke kalaman da ba su dace ba da gurbata tarbiya.
Hukumar ta fara tattaunawa da kamfanın TikTok domin lalabo hanyoyin dakile barnar da matasan ke yi ta hanyar sanya wasu ka’idoji domin rage badala.
Saurari cikakken hirar hukumar Hisbah da Baraka Bashir:
Dandalin Mu Tattauna