Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Ta Bullo Da Wani Shirin Tsaro Mai Taken ''OP VELVET''


Nigeria Police Force Logo
Nigeria Police Force Logo

Biyo bayan kalubalen tsaro da ya dabaibaye yankin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriyua, rundunar ‘yan sandan birnin ta bullo da wani shirin samar da tsaro mai taken operation VELVET da a cikinsa ake fatan samun sauki.

ABUJA, NIGERIA - Shirin na OP VELVELT da kwamishinan ‘yan sanda CP Ben Igwe ke jagoranta da kansa, na kai samame da hare-hare ne a maboyar miyagu dake sassa daban-daban na birnin.

A irin wannan samame na baya-bayan nan ne kwamishinan ‘yan sandan ya jagoranci kai samame a wani gidan dambe dake unguwar Dei Dei da ke wajen birnin Abuja inda aka cafke kimanin mutane dari uku.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Abujan ta ce an sami makamai da miyagun kwayoyi daga wurin wasu da ga cikin mutanen da aka kama.

Ta ce za a tantance wadanda ake ganin ko zargin masu laifi ne don daukar mataki na gaba, wanda bai da laifi kuma a sallame shi.

Dama dai mutanen garin yankin sun dade suna korafi da nuna fargabar barazanar tsaro ganin nau'o'in mutanen dake tattaruwa a wannan gidan damben.

Amma masana tsaro irin su Dr. Kabiru Adamu na ganin ko da yake wannan mataki ne mai kyau amma rashin daukar matakan hukunta duk wanda aka samu da laifi a irin wannan mataki ba karamar koma baya bane.

Saurari cikakken rahoto daga Hassan Maina Kaina:

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Ta Bullo Da Wani Shirin Tsaro Mai Suna VELVET.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG