Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ra’ayoyin Masana Akan Ficewar Kasashen Nijar, Mali Da Burkino Faso Daga ECOWAS


Mali Niger Burkina Faso ECOWAS
Mali Niger Burkina Faso ECOWAS

Najeriya ta yi Allah Wadai da ficewar Jumhuriyar Nijar, Mali da Burkina Faso daga Kungiyar ECOWAS ko CEDEAO duk da cewa ya zuwa yau Kungiyar ta ce ba ta samu wata sanarwar ficewar kasashen ba.

ABUJA, NIGERIA - A wata sanarwa da ke dauke da sa hannun kakakin Ma'aikatar Harkokin Kasashen Wajen Najeriya, Francisca Omayuli ta nuna cewa ma'aikatar tana marawa Kungiyar ECOWAS baya, inda ta ce Kungiyar ta yi namijin kokari wajen ganin an samu zaman lafiya da wadata da dorewar dimokradiya a yankin Afirka ta Yamma a tsawon rabin karni.

Omayuli ta ce Najeriya na goyon bayan Kungiyar ECOWAS din ne domin jadadda tsarin da ya dace da kuma hada karfi da karfe wajen kare yanci da walwalar daukacin ‘yan kasashen mambobin kungiyar 15.

Omayuli ta kara da cewa Najeriya ta yi aiki da gaskiya da aminci don tuntubar dukkan yan uwa na kungiyar don magance matsalolin da ake fuskanta.

To saidai kwararre a fanin diflomasiyar kasa da Kasa kuma Malami a Jami'ar Abuja, Dr. Farouk Bibi Farouk, ya yi nazari cewa fitar wadannan kasashe daga Kungiyar ECOWAS ba alheri ba ne, ba kuma tsari ba ne na diflomasiya mai kyau, domin idan an duba tarihin da ke tsakanin Nijar da Najeriya da aka yi shekaru aru-aru ana yi zai zama kaman ba a taba yin sa ba.

Yanzu zai zama abu ne da za a zo ana cin duduniyan juna ana farraka zamantakewa da juna, kuma hakan ba alheri ba ne ga kasashen duka.

Shi ma shugaban Kungiyar Amnesty International a Najeriya, Auwal Musa Rafsanjani, ya yi tsokaci cewa kasashen da suka dauki wannan mataki, kasashe ne masu cin gashin kansu kuma suna da ‘yancin shiga ko fita daga ko wace kungiya ba tare da wani laifi ba.

Rafsanjani ya ce shugabanin Kungiyar ECOWAS su ne suka ja aka shiga wanan hali, domin abinda ya ba kasashen haushi shi ne takunkunmi da aka kakaba masu, wanda ya ja wa kasashen koma baya a fanoni da yawa, saboda haka suna ganin kaman an ci zarafin su ne, ba tare da an nuna masu wani zumunci ko mutunci ba.

To ga shugaban Kungiyar Matasa mai suna AJEPA ta kasar Nijar, Lauoli Tsalha ya ce an samu wannan baraka ne domin wadannan kasashe guda uku sun kwashi lokaci mai tsawo a wani hali na kakanakayi amma CEDEAO ko ECOWAS ba ta taba taimaka wa kasashen ba, sanan kuma ECOWAS ta kakaba wa kasashe takunkunmi masu tsanani ba tare da kula da yanayin da al'ummar kasashen suke ciki ba.

Laouli ya yi kira ga ECOWAS cewa ta dubi kanta, domin abinda ta ke yi kokawa ce da kasashen da ke cikin ta, ba tare da bin ka'idojin da suka kafa kungiyar ba.

Ya kara da cewa ya kamata manya su dauki mataki domin a yi sulhu, domin shi ne abinda ya fi a'ala ga Kungiyar baki daya.

Abin jira a gani shi ne irin matakin da kungiyar ECOWAS za ta dauka idan ta samu sanarwar ficewar kasashen na Nijar, Mali da kuma Burkina Faso daga kungiyar mai kunshe da kasashe 15 daga Afirka ta yamma.

Saurari cikakken rahoto daga Medina Dauda:

Ra’ayoyin Masana Akan Ficewa Kasashen Nijar, Mali Da Burkino Faso Daga ECOWAS.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:58 0:00

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG