Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Yankuna A Zamfara Na Fargabar Kwararowar ‘Yan Bindiga Daga Yankunan Da Aka Fatattakesu


Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal
Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal

Yayin da al'ummomin wasu yankunan Najeriya ke farin ciki a kan matakan da mahukunta suka dauka wadanda suke fatar su kawo sauki ga matsalar rashin tsaro, wasu kuwa fargaba ce ta karu gun su domin suna ganin barayin zasu kwararo yankuan su ne daga yankunan da aka dauki matakan.

ZAMFARA, NIGERIA - Wannan na zuwa ne a lokacin da jihar Zamfara dake Arewa maso yammacin Najeriya ta kaddamar da Askarawan Zamfara wadanda zasu fafata da 'yan bindiga, inda makwabtan Zamfarar ke kara samun fargaba.

Matsalar rashin tsaro dai ta jima tana daidaita yankunan Arewacin kasar, yanzu mahukunta a Arewa maso yamma sun samu hadin kai na kawar da ita, kamar yadda jihohin Katsina da Zamfara suka kafa rundunar tsaro ta sa kai.

Gwamnan jihar Katsina Umar Dikko Radda ya ce ba shakka sai sun ga bayan 'yan ta'adda a koi'na cikin yankin arewa maso yamma lokacin da yake jawabi a jihar Zamafara wurin kaddamar da rundunar tsaron ta sa kai.

To sai dai bayan da jihar Zamfara ta kaddamar da jami'an sa kai a ranar laraba ta wannan mako, al'ummomi da ke makwabtaka da jihar sun ce akwai yiwuwar 'yan ta'adda su kara kwararowa zuwa yankunansu idan suka ji matsi a jihar Zamfara bayan kuma an fargago su daga Katsina.

Bashir Altine Guyawa Isa na daga cikin masu bibiyar lamarin tsaro a Najeriya kuma dan asalin yankin Isa ne mai makwabtaka da jihar Zamfara, yace koma lokacin da aka kafa irin wannan runduna a jihar Katsina Barayi sun yi kaka-gida a jihar Zamfara.

Yankin Danko Wasagu na jihar Kebbi ma ya yi iyaka da jihar ta Zamfara kuma mutanen wannan yankin sun nuna fargaba har da kara yin kira ga gwamnatin jihar Kebbin.

To wadanne matakai mahukuntan wadannan jihohin suka dauka na kawar da fargabar jama'arsu, Gwamnan Sakkwato Ahmad Aliyu Sokoto yace suma ba a bar su a baya ba wajen kafa irin wannan rundunar domin yanzu haka jami'an da gwamnatinsa ta dauka suna kan karbar horo.

Ita kuwa gwamnatin jihar Kebbi ba ta ayyana daukar irin wannan mataki ba amma dai gwamna Nasir Idris ya fito da shirin karfafawa jami'an banga inda har ya samar musu baburan aikin taimakawa jami'an tsaro.

Wadannan matakan dai acewar masana tsaro sun dace muddin za a tabbatar da yin cikakken amfani da su, domin samar da tsaro a yankunan da ke fama da matsalolin rashin tsaro.

Saurari cikakken rahoto daga Muhammad Nasir:

Wasu Yankuna A Zamfara Na Fargabar Kwararowar ‘Yan Bindiga Daga Yankunan Da Aka Fatattakesu.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:35 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG