Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Kalubalanci Hukumar EFCC Ta Kara Kaimi Kan Yakin Damfara Ta Intanet


Shugaban Kasan Najeriya, Bola Tinubu
Shugaban Kasan Najeriya, Bola Tinubu

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya kalubalanci hukumar EFCC, mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, data kara kaimi a yakin da take yi da annobar damfara ta hanyar amfani da kafar sadarwa ta intanet da sauran nau'ukan almundahana.

A larabar data gabata ne, Shugaba Tinubu yayi wannan kiran a yayin gabatar da wata makala ga matasa a Abuja mai taken: "addini da yaki da karbar rashawa" tare da kaddamar da shirin bin diddigi da takaita almundahana a hukumomi da ma'aikatun gwamnati da hukumar EFCC ta shirya.

Tinubu yayi kuma tsokaci akan cewar damfarar intanet ta zamo wata annoba data bata sunan Najeriya a idon duniya, don haka wajibi ne EFCC ta bullo da sabbin dabarun maganceta yadda ya dace,

"Kasarmu bata 'yan damfara kuma shugaben da ake yiwa laifuffukan intanet da "damfara 'yar najeriya" bai dace ba kuma abu ne da bazamu lamunta ba. Al'amarin laifuffukan yanar gizo wata annoba ce data zamo ruwan dare gama duniya” in ji Shugaba Tinubu.

Ya kara da cewa “dukkanin al'amuran duniya a yanzu sun koma ta kafar sadarwar intanet. Harkar gwamnati da kasuwnci da tafiyar da hukumomi harma da harkokin iyalin jama'a duk sun koma dogaro akan intanet. Don haka matsalar 'yan damfarar intanet barazana ce ka ilahirin duniya”.

Tinubu ya ci gaba da cewar , "wannan dalili ne yasa bai kamata a saurara wajen yaki da wannan annoba. Zan so in baiwa EFCC tabbacin cewar gwamnati zata ci gaba da dafa mata a kokarin da take yi na ganin bayan wannan mummunan al'aamari.

Tinubu wanda ya bayyana hakan ta bakin Mataimakinsa Kashim Shettima, ya bayyana aniyar gwamnatinsa na daukar tsauraran matakan magance matsalar cin hanci da rashawa, inda ya jaddada cewar babu yadda za'a yi mu maida hankulanmu kan bunkasa kasa a yayin da cin hanci da rashawa ke kara samun gindin zama."

"Babu wata kasa da zata samu ci gaba matukar bata karya lagon matsalar cin hanci da rashawa ba. An umarci hukumar EFCC ta gudanar da aikinta ba tare da nuna sani ko sabo ba. Ajandar gwamnatinmu na sabuntawa 'yan Najeriya irin burin da suke da shi na samun sahihiyar ba zai yi wasarere da batun yaki da rashawa ba. Ya kamata mu hada karfi da karfe domin nemawa najeriya sabuwar makoma.

Tinubu ya kara yiwa EFCC kaimi akan kada ta bari maganganun wasu mutane akan yakin da take ci gaba da kaddamarwa akan matsalar damfarar intanet da sauran nau'ukan almundahana, inda yace gwamnati tana sane da irin yarfe da kagen da ake yi mata akan kokarinta na hukunta 'yan damfarar. Ba zamu zura ido muna kallon matasa na ci gaba da aikata muggan laifuffuka ba”.

Shugaban Hukumar Yaki da masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) Ola Olukoyede
Shugaban Hukumar Yaki da masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) Ola Olukoyede

A jawabinsa yayin bude taron, Shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukayode, waiwaye yayi akan namijin kokarin da hukumar tayi a bangaren gurfanarda masu laifi tare da kwato kadarorin da aka wawure.

Domin magance matsalar, Shugaban Hukumar EFCC ya bukaci a maida hankula kan daukar matakan rigakafin dakile laifuffuka ta hanyar fitar da sahihan dabarun da zasu taimakawa kokarin hukumar.

Yace “Hakika, daukar matakan rigakafi da sahihan manufofi akan matsalar cin hanci da rashawa ce hanyar mafi dacewa wajen tabbatar da tsaron al'umma da bunkasa tattalin arziki da kuma gudanar da ma'aikatun gwamnati dana masu zaman kansu yadda ya dace.

“Daidata dabarun rigakafin wani yunkuri ne na dabbaka matakan jinkirta daukar mataki tafiya da kowa a bangaren mu'amalantar masu ruwa da tsaki.

“Ya ci gaba da cewar, manufarmu ita ce lalubo hanyoyin dakile cin hanci da rashawa a hukumomi da ma'aikatu a gwamnati ko kamfanoni masu zaman kansu kafin a gurfanar dasu”.

Shugaban Hukumar EFCC ya kara da cewar, zasu maida hankali a bangarori 2 masu mahimmanci da suka hada da shigar da matasa cikin harkar tsaftace kafar intanet da yin awon gaba da matsalar cin hanci daga hukumomi da ma'aikatun gwamnati.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG