Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ba Ta Goyon Bayan Boko Haram - Jakada Mills


Jakadan kasar Amurka a Najeriya, Richard Mills
Jakadan kasar Amurka a Najeriya, Richard Mills

Mista Mills ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan gabatar da jawabinsa ga Kungiyar Gwamnonin Najeriya NGF. A jawabin bayan taron na su, kungiyar ta ce har yanzu akwai alaka mai karfi tsakanin Najeriya da kasar Amurka.

Jakada Richard Mills ya ce an tabbatar da samar da ingantattun tsare tsare don ganin taimakon da Hukumar USAID ke bayarwa ya kai ga wadanda ake so. Mills ya ce an ayyana Boko Haram a matsayin Kungiyar ta'addanci ta kasashen waje tun a shekara ta 2013, saboda haka zai yi wuya Hukumar USAID ta yi wata alaka da su.

Mills ya kara da cewa babu wata kawar Najeriya da ta fi Amurka dagewa wajen yin Allah waddai da ta'addancin Boko Haram. Mills ya ce babu wata shaida da ta nuna cewa hakan yana faruwa, kuma tabbas, da a ce mun taba samun shaidar da aka gabatar wa Amurka cewa ana karkatar da kudaden hukumar zuwa ga Boko Haram, nan take za mu yi bincike tare da abokan mu na Najeriya in ji kakada Mills.

To sai dai duk da wannan tabbaci da Jakada Mills ya bada, Majalisar Wakilai ta kafa wani kwamiti mai karfi da zai yi bincike kan wannan batun kamar yadda Dan Majalisar Wakilai daga Yamaltu Deba ta Jihar Gombe Inuwa Garba ya shaida mani inda ya ce daga shekara 2022 zuwa 2024 hukumar USAID ta shigo da kudi wuri na gugar wuri dalar Amurka biliyan 2.7 amma babu abinda wadannan kudade suka tsinana wa mabukata, domin a wasu wurare mutane na zaune a gindin bishiya suna gudun hijra; wasu suna zaune a matsayin an kashe mazajensu; yara suna tare a matsayin marayu an kashe masu iyayen su; wasu suna zaune a daidai wanan lokaci da muke magana ba su karya ba - babu abinci, babu wurin kwana, ba makaranta, ba ruwan sha, ba hanya, babu komi na bawa al'umma karfin gwiwa.

Inuwa ya ce ana neman wuta a makera amma ta tashi a masaka, saboda haka Inuwa ya ce yana ganin binciken zai bijiro da abubuwa dayawa.

Jakada Richard Mills dai ya ce burin kasar Amurka shi ne karfafa dangantaka tsakanin ta da Najeriya a fannoni daban daban na rayuwa domin ganin an samu cigaba mai dorewa.

Saurari cikakken rahoton Madina Dauda:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG