Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Na Farautar Bello Turji Ruwa A Jallo - Babban Hafsan Sojin Najeriya

Babban Hafsan Sojin Najeriya, Laftanar Janar Olufemi Oluyede

Babban Hafsan Sojin Najeriya, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya ce dakarun sojin kasar sun dukufa wajen farautar fitaccen shugaban ‘yan bindigar nan Bello Turji kuma bada jimawa ba zasu gama da shi.

Da yake magana yau Alhamis a hedikwatar Rundunar tabbatar tsaro a yankin Arewa maso yammacin Najeriya da aka yi wa lakabi da “Operation Fasan Yamma”, laftanar janar Olufemi Oluyede ya sha alwashin cewa kwanakin da suka ragewa Turji a duniya kidayayyu ne, yana mai jaddada cewa tuni manyan ‘yan bindigar suka arce kuma yanzu haka dakarun soji na nema ruwa a jallo.

Babban Hafsan Sojin Najeriya, Laftanar Janar Olufemi Oluyede a hedikwatar Rundunar tabbatar tsaro a yankin Arewa maso yammacin Najeriya

“Kuma rundunar soji na ci gaba da aiki ba bu kama hannun yaro wajen tabbatar da tsaron jihar Zamfara da Arewacin kasar.” Inji shi.

Yace Bello Turji yanzu haka ya can Yana boyo kuma duk inda ya shiga za su zakulo shi, yace Turji zai iya ci gaba da gudu, amma ya sani lokaci ya kure mashi.

Babban Hafsan Sojin Najeriya, Laftanar Janar Olufemi Oluyede a hedikwatar Rundunar tabbatar tsaro a yankin Arewa maso yammacin Najeriya
Babban Hafsan Sojin Najeriya, Laftanar Janar Olufemi Oluyede a hedikwatar Rundunar tabbatar tsaro a yankin Arewa maso yammacin Najeriya

Babban Hafsan sojin wanda yayi karin haske kan nasarorin da aka samu a baya-bayan nan akan yaki da Yan bindigar ya bayyana cewa sojojin Najeriya sun kashe manyan shuwagabannin‘yan bindiga da Dama wadanda suka hada da Kachalla Dan bokkolo, Kachalla Samaila, da Kachalla Boderi.

Babban Hafsan Sojin Najeriya, Laftanar Janar Olufemi Oluyede a hedikwatar Rundunar tabbatar tsaro a yankin Arewa maso yammacin Najeriya
Babban Hafsan Sojin Najeriya, Laftanar Janar Olufemi Oluyede a hedikwatar Rundunar tabbatar tsaro a yankin Arewa maso yammacin Najeriya

Duk da yake Laftanar janar Olufemi yace suna sane da kalubalen da sojoji ke fuskanta, yace suna kan daukar matakai don shawo kan su. Daga nan sai ya bukaci ‘yan Najeriya da su taimakawa jami’an tsaro ta hanyar ba da bayanan da suka dace a kan lokaci don taimakawa ayyukan soji.

Babban Hafsan Sojin Najeriya, Laftanar Janar Olufemi Oluyede a hedikwatar Rundunar tabbatar tsaro a yankin Arewa maso yammacin Najeriya
Babban Hafsan Sojin Najeriya, Laftanar Janar Olufemi Oluyede a hedikwatar Rundunar tabbatar tsaro a yankin Arewa maso yammacin Najeriya

Wannan ziyarar dai ita ce ta farko da Babban Hafsan sojin ya kai a jihar Zamfara tun bayan hawansa akan mukamin a ranar 30 ga watan Oktoba, 2024.

~Abdulrazak Bello Kaura~

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG