Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Jana'izar Jami’an Tsaro Da ‘Yan Bindiga Suka Kashe A Jihar Sakkwato


Jana’izar Jami’an Tsaro 6 Da Wasu ‘Yan Bindiga Suka Kashe A Jihar Sakkwato
Jana’izar Jami’an Tsaro 6 Da Wasu ‘Yan Bindiga Suka Kashe A Jihar Sakkwato

Matsalar rashin tsaro na ci gaba da tayar da hankulan jama'a a Arewacin Najeriya, duk da yake kwanan nan jami'an tsaro na cewa suna samun galaba ga yaki da 'yan ta'adda

Ko a jiya Laraba sai da aka yi jana'izar wasu jami'an tsaro na al'umma da gwamnatin Sakkwato ta samar don taimaka wa lamarin tsaro, wadanda 'yan bindiga suka yi wa kofar rago suka buda musu wuta.

Kawar da matsalar tsaro a Najeriya na ci gaba da gagara, domin ko an samu sauki sai matsalar ta juyo ta haddabi jama'a tare da salwantar da rayuka.

Wannan karo 'yan bindiga ne suka yi wa jami'an tsaron al'umma kofar rago, lokacin da jami'an ke kan babura a yankin Sabon Birni na gabashin Sakkwato yankin da ya jima yana fama da matsalar rashin tsaro.

Wani mazaunin yankin ya sheda wa Muryar Amurka cewa matsalar ta auku ne lokacin da jami'an ke kan hanya a kan babura su kadai ba tare da sauran jami'an tsaron soji da MOPOL da suka saba yin aiki tare ba.

Dan majalisar yankin Sabon Birni ta yamma ,yankin da lamarin ya faru, Aminu Almustapha Boza ya nuna takaici a kan faruwar lamarin wanda yace ya faru ne saboda ja da baya daga aikin da aka soma na yakar 'yan bindiga.

Yanzu haka akwai al'ummomi da 'yan bindiga suka dorawa biyan kudi miliyan ashirin da biyar a kan kowane gari, acewar dan majalisar.

Rundunar 'yan sandan Najeriya, ta bakin kakakinta a Sokoto DSP Ahmad Rufa'i tace tana kan bincike a kan wannan batun.

Saurari cikakken rahoto daga Muhammadu Nasir:

‘Yan Bindiga Sun Kashe Jami’an Tsaro 6 A Jihar Sakkwato.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG