Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kwace $4.7M Daga Hannun Emefiele

Tsohon Shugaban Babban Bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele
Tsohon Shugaban Babban Bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele

A hukuncin da ya zartar yau Juma’a, Mai Shari’a Yallim Bogoro ya kuma ba da umarnin kwace jarin dala 900, 000 da ake alakantawa da wata ‘yar uwar Emefiele, Anita Joy Omolie, a mataki na dindindin.

Babbar kotun tarayya da ke Legas ta ba da umarnin kwace dala miliyan 4 da 700 da naira miliyan 830 da kuma kadarori da dama da ake dangantawa da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, a mataki na dindindin.

A hukuncin da ya zartar yau Juma’a, Mai Shari’a Yallim Bogoro ya kuma ba da umarnin kwace jarin dala 900, 000 da ake alakantawa da wata ‘yar uwar Emefiele, Anita Joy Omolie, a mataki na dindindin.

Haka kuma kotun ta ba da umarnin karshe na kwace wani jarin dala miliyan 4.4 da ake alakantawa da kamfanin Blue Energy Services LTD da wasu naira miliyan 283 da ke ajiya bankin Zenith da ake dangantawa da kamfanin Liman Investment LTD da wasu fam 20, 000 da fam 1, 999, 50 da ake alakantawa da kantin canjin kudade na Exactquote (BDC), kuma dukkanin kamfanonin na da alaka da Omolie.

Kamar yadda hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya ta’annati ta nema, Mai Shari’a Bogoro ya amince da kwace dukkanin kudaden a matakin karshe tare da mayar da su ga gwamnatin tarayyar kasar bayan da yace an samesu ne ta haramtacciyar hanya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG