Jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya na daga cikin wuraren da ake samun wannan matsalar abin da gwamnan jihar ta tallaka da cewa 'yan bindigar na zuwa ne daga makwabtan jihohi.
Matsalar rashin tsaro a yankin arewacin Najeriya ta kasance tamkar kulli gagara kwanta, domin ko ta tafi sai ta waiwayo bayan dan lokaci.
Jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya na daga jihohin da mahukunta kefadi-tashi wajen kawar da matsalar amma kuma ko ta tafi sai ta dawo.
Alal misali a yankin gabashin Kebbi haujin Argungu inda Lakurawa suka saba kai hari a garin Mera, ba da jimawa ba an samu wasu hare-hare a garin Natsini da nabaya-bayannan a garin Gulma inda har da mata 'yan bindiga suka sheke ayar su.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ma ta hannun kakakinta a jihar Kebbi CSP Nafi'u Abubakar ta fitar da jerin rubutattun bayanai inda ta tabbatar da wani hari a yankin Suru inda har jami'anta suka kashe 'yan bindiga 4, da kuma wasu makiyaya da ta kama su 47 da take tuhuma da yunkurin aikata ta'addanci.
Rundunar tace sun turo dabbobi fiye da 300 suka mamaye harabar gidajen ma'aikatan kwalejin kimiya da fasaha ta Waziri Umaru har sun sassare wani mai suna Abdullahi Muhammad Idris, hakama ta kama wasu matsafa da mahara duk kusan lokaci daya.
Ko a wannan mako sai da wasu 'yan bindiga suka kai hari ga wani fitaccen dansiyasa, Umar Nashaya Diggi, duk yake Allah Ya tsirar da shi, ya yi magana a ka harin da aka kai masa.
Duk wadannan suna faruwa ne yayin da gwamnatin jihar ta Kebbi ke aiki tare da gwamnatin Najeriya wajen kawar da matsalar ta rashin tsaro daga jihar, sai dai gwamnan jihar Kwamred Nasir Idris ya nuna takaici a kan yadda matsalolin ke waiwayowa.
Rundunar tsaron ta sojin Najeriya ta sha bayyana cewa jami'nta na aiki tukuru domin kawar da ayukkan 'yan bindiga daga jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara.
Dukan fatar jama'a dai ba za ta wuce ganin an samu wanzuwar zaman lafiya ba domin rayuwa ta gudana cikin walwala da salama.
Saurari cikakken rahoto daga Muhammadu Nasir:
Dandalin Mu Tattauna