Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MKO Abiola Ne Ya Lashe Zaben 12 Ga Watan Yunin 1993 - IBB


MKO Abiola (hagu) da Ibrahim Babangida
MKO Abiola (hagu) da Ibrahim Babangida

An soke zaben tun gabanin a ayyana wanda ya samu nasara.

Shekaru 32 bayan daya soke zaben shugaban kasa na 12 ga watan Yunin 1993 mai ciki da cece kuce, a karon farko tsohon shugaban mulkin sojan Najeriya, Ibrahim Babangida, ya amince da cewar barden dimokiradiya mai taimakon al’umma Moshood Kashimawo Olawale (MKO) Abiola ne mutumin da ya lashe zaben.

Wannan labari na kunshe ne a cikin littafin tarihin rayuwar Babangidan mai shafuka 420, mai taken “Journey In Service” a turance, wanda aka kaddamar a Abuja a yau Alhamis da ya tattaro mahalarta daga ciki da wajen Najeriya.

Manazarcin littafin, tsohon mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo, yace lakanonin da ake yiwa Babangidan na “evil genius” da “maradona” sun amsa tambayar ko Abiola ne ya lashe zaben 12 ga watan Yuni ko akasin hakan a littafin nasa.

“Duk da cewa na taba fadar cewa akwai yiyuwar ba Abiola bane ya lashe zaben, amma bayan zurfin tunani, tare da nazarin dukkanin bayanan da ke akwai, musamman cikakken sakamakon zaben wanda aka wallafa a sharhin dake karshen littafin nan, babu shakka cewar MKO Abiola ne ya lashe zaben 12 ga watan Yuni,” kamar yadda Babangida ya amince a cikin littafinsa.

A shekarar 2018, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sauya bikin ranar dimokradiyyar daga 29 ga watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni domin karrama Abiola tare da tunawa ‘yan Najeriya game da zabe mafi sahihanci a tarihin kasar.

An ware ranar ne da nufin murnar akidun tsarin dimokradiyya tun daga farkon jamhuriya ta 4 shekaru 25 da suka gabata

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG