Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babu Hujjar Da Ke Tabbatar Da USAID Ce Ke Daukar Nauyin Boko Haram A Najeriya-Jakadan Amurka


Jakadan kasar Amurka a Najeriya, Richard Mills
Jakadan kasar Amurka a Najeriya, Richard Mills

A ranar 13 ga watan Febrairun da muke ciki ne, dan Majalisar Dokokin Amurka, Scott Perry, ya zargi USAID da daukar nauyin kungiyoyin ‘yan ta’adda, ciki harda Boko Haram.

Jakadan kasar Amurka a Najeriya, Richard Mills, yayi watsi da zargin cewar hukumar raya kasashe ta Amurka (USAID) ce ke daukar nauyin Boko Haram ko sauran kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Mills wanda ya gana da mambobin kungiyar gwamnonin Najeriya a Abuja a daren jiya Laraba yace, babu wata hujja dake tabbatar da zargin.

Ya kara da cewar babu kasar data fi amurka sukar tashe-tashen hankalin da boko haram ta haddasa, inda ya bada tabbacin cewar da zarar an samu hujjar, gwamnatin amurka zata yi aiki tare da takwararta ta najeriya domin bankado ta.

“ko kadan babu wata hujja game da irin wannan karkatarwar, idan har muka samu hujjar cewar ana karkatar da kudaden daukar nauyin wani shiri, ba zamu yi kasa a gwiwa ba wajen bincika hakan tare da kawayenmu na Najeriya,” a cewar Mills.

A ranar 13 ga watan Febrairun da muke ciki ne, dan Majalisar Dokokin Amurka, Scott Perry, ya zargi USAID da daukar nauyin kungiyoyin ‘yan ta’adda, ciki har da Boko Haram.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG