Kwamitin Majalisar Wakilan Najeriya akan gyaran kundin tsarin mulki ya yi fatali da dukkanin shawarwari 31 na kirkirar jihohi, inda yace sun gaza cimma bukatun tsarin mulki.
Majalisar ta karbi shawarwarin game da kirkirar sabbin jihohi 31 a ranar 6 ga watan Fabraitun da muke ciki.
Sai dai, Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilan, Benjamin Kalu, ya ba da sanarwar cewa babu ko guda daga cikin bukatun kirkirar jihohi a Najeriyar da ta dace da bukatun kundin tsarin mulkin da har za’a duba ta.
Kalu, wanda ke jagorantar kwamitin majalisar a kan gyaran kundin tsarin mulkin 1999, ya bayyana hakan a yau Juma’a yayin wani taron nazarin manufa na yini 2 a garin Ikot Ekpene na jihar Akwa Ibom.
Majalisar Wakilai ta 10 da hadin gwiwar cibiyar fafutukar sauyin dokoki da manufofi ta PLAC da tallafin ofishin raya kasashen renon ingila na Burtaniya (FCDO) ne suka shirya taron.
Manufar sa ita ce nazarin shawarwarin a kan gyaran kudin tsarin mulki tare da tantance mataki na gaba a kan tsarin nazarin.
Dandalin Mu Tattauna