Karin cajin cirar kudi a ATM da Gwamnatin tarayya ta aiwatar, wanda a baya yake a matsayin ₦35, yanzu zai koma ₦200 har zuwa ₦500, ya jawo cece-kuce tsakanin ƴan kasar.
'Ƴan kasar dai na ci gaba da kokawa bisa yadda Gwamnatin kasar ke ci gaba da kakaba musu sabbin haraji.
Masana tattalin arziki dai na ganin hakan wata barazana ce ga talakawan kasar da kudin shigar su bai taka kara-ya-karya ba, kuma hakan zai sa 'ƴan kasar su kaurace wa ajiye kudadensu a bankuna.
Daga Abuja, Wakiliyar Mu Rukaiya Basha ta aiko mana da cikakken rahoton.
A wata sanarwar da sashin sadarwar babban bankin Najeriya CBN ya fitar, babban bankin ya umurci dukkanin bankuna da cibiyoyin kudi na kasar da su aiwatar da sabon tsarin cajin kudi na ₦200 a duk adadin kudin da ya kai ₦20,000 da aka cire a na’urorin cirar kudi na bankuna (ATM) kuma umarnin zai fara aiki ne ranar 1 ga Maris din shekarar da muke ciki.
A cewar babban bankin, sabon tsarin cajin kudin na ATM ya zamo musu tilas ne, idan akayi la’akari da yadda hauhawar farashin gudanar ayyuka da kuma hada-hadar kudade ya karu a kasar, sai kuma bukatar kara inganta yadda ayyukan na ATM suke.
Sanarwar ta kara da cewa, tsarin cajar kudin na ATM din, zai shafi wanda su ka yi huldar cirar kudin a ATM din bankunan da basa hada-hadar kudade tsakanin su, sai dai bankin ya kara da cewa, ba za a caji ko da sisin kobo ba, ga wadanda su ka yi huldar cirar kudi a bankunan da suke hada-hada.
'Ƴan kasar dai na bayyana rashin jin dadin su game da wannan sabon tsari.
Ko ya masharhanta lamurran yau da kullum ke ganin sabon tsarin na CBN, Imrana Wada Nas da ke matsayin shugaban kungiyar rundunar talakawan kasar na mai goyon bayan masu kokawa kan karin harajin na ATM.
Dr. Isa Abdullahi Kashere da ke nazartar harkar tattalin arziki a jami’ar tarayya ta Kashere a Jihar Gombe, na ganin wannan sabon tsarin haraji ka iya kawo wa tattalin arzikin kasar nakaso.
Yanzu abin jira a gani shi ne yadda gwamnatin kasar za ta aiwatar da sabbin ayyukan ci gaba a kasar, bayan kare-karen haraji da ta bijiro da su.
Saurari cikakken rahoton Rukaiya Basha:
Dandalin Mu Tattauna