Kamfanin samarda hasken lantarki na Najeriya (TCN) ya bayyana cewa za’a samu daukewar hasken lantarki na sa’o’i 7 a wasu sassa na birnin tarayyar Najeriya, Abuja.
A sanarwar da ya fitar, babbar manajan TCN a kan huda da jama’a, Ndidi Mbah, tace sassan da al’amarin zai shafa zasu fuskanci daukewar lantarkin ne a ranaikun Asabar 22 da Lahadi 23 ga watan Fabrairun da muke ciki, tsakanin karfe 9 na safe zuwa 4 yamma a kowace rana.
Ta alakanta lamarin da gyare-gyaren da aka saba yiwa wasu transfomomi 2 a duk shekara domin rigakafin lalacewarsu.
Daukewar lantarkin na sa’o’i 7 zai shafi babban asibitin kasa, da tashoshin rarraba lantarkin na G2 injection dake unguwanni Garki da Area 1 da kuma Asokoro.
Sauran sassan sun hada da unguwar rukunin gidajen ‘yan majalisu ta Apo da Apo Resettlement da Gudu da Apo Mechanic da unguwannin da ke kewaye dasu.
Kamfanin na TCN ya nemi gafarar al’umma akan rashin jin dadin da daukewar lantarkin zai jefa kwastomomin a wannan dan tsakani.
Dandalin Mu Tattauna