Kafaffen yada labaran cikin kasar Najeriya sun ruwaito cewar Shugaban na Sengal ya zo ziyarar aiki a Najeriya ne.
Ana zargin wani matashi, Shafi'u Abubakar, wadda aka ruwaito cewar, ya bayyana wata dadaddiyar takaddamar rabon gado a matsayin dalilinsa na haddasa fashewar.
A daidai lokacin da duniya ke komawa fannin amfani da iskar gas don rage illolin sauyin yanayi ga al’umma, gwamnatin Najeriya ta kaddamar da muhimman ayyukan samar da iskar gas guda uku a jihohin Imo da Delta.
Shugaban Kungiyar Kwadago ta NLC, Joe Ajero, ya bayyana cewar ba da gaske gwamnatin tarayyar take ba a tattaunawarta da 'yan kwadagon game da sabon mafi karancin albashi.
Rundunar yan sanda ta jihar Kano tace ta kama wani matashin daya cinna wuta a wani masallaci yayin da masu ibada ke sallar asuba yau Laraba a garin Larabar Abasawa na karamar hukumar Gezawa.Kimanin mutane 35 al'amarin ya shafa kuma suna karbar magani a Asibitin kwararru na Murtala dake birnin Kano.
Kamfanin Flynas ne ake sa ran zai dauki alhazan na jihar Kebbi a ranar Laraban nan. Sauran jihohin da kamfanin na Flynas zai yi jigilar su zuwa kasar ta Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2024 sun hada da jihohin Ikko (Lagos), Osun, Ogun, Borno, Niger, Sokoto, Yobe da Zamfara.
Emefiele ya musanta zargin ne a yau Laraba yayin da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta gurfanar da shi a gaban mai shari’a Maryann Anenih na babbar kotun babban birnin tarayya Abuja, bisa tuhume-tuhume hudu.
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta dakatar da harajin yanar gizo mai cike da cece-kuce a hada-hadar bankunan na'ura mai kwakwalwa.
‘Yan Najeriya sama da miliyan daya ne suka mika takardar neman sabon tsarin basussuka, inji gwamnatin tarayya a ranar Talata.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.