Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Emirates Zai Koma Jigila Tsakanin Legas Da Dubai A Ranar 1 Ga Watan Oktoba


Jiragen kamfanin Emirates
Jiragen kamfanin Emirates

Kamfanin jiragen saman Emirates ya bayyana cewar zai cigaba da ayyukansa a Najeriya tun daga ranar 1 ga watan Oktoba mai zuwa, inda zai fara zirga-zirga tsakanin biranen Legas da Dubai a kullum.

A sanarwar daya fitar a yau Alhamis, kamfanin jiragen saman, dake da tushe a Hadaddiyar Daular Larabawa, ya bayyana cewar zai cigaba da jigila ne da jirgi samfurin boeing 777-300er.

Mataimakin Shugaban Kamfanin na Emirates kuma babban jami’in kasuwancinsa, Adnan Kazim yace, “muna murnar dawowa harkoki a Najeriya. a bisa al’ada jigilarmu ta Legas zuwa Dubai ta shahara tsakanin abokan huldarmu na Najeriya kuma muna fatan mu cigaba da jigilar dukkanin rukunin fasinjojinmu zuwa Dubai da kuma fiye da wurare 140 da jiragenmu ke zuwa.

“Muna godiya ga gwamnatin Najeriya saboda hadin gwiwa da tallafinta wajen sake dawo da wannan zirga-zirga sannan muna fatan sake marabtar fasinjoji a jiragenmu.”

Kamfanin jiragen saman Emirates ya dakatar da zirga-zirga tsakanin Legas da Dubai a shekarar 2022 sakamakon gaza fitar da kudadensa da suka makale a hannun gwamnatin Najeriya biyo bayan wata takaddamar diflomasiya tsakanin kasashen biyu.

Najeriya da Hadaddiyar Daular Larabawa nada dadadden tarihin hana zirga-zirgar jiragen sama a tsakaninsu sakamakon wasu takaddamomi da suka baibaye yarjejeniyar kasa da kasa akan sufurin jiragen sama (basa). Daga bisani kuma wata takaddamar ta sake kunnu kai akan bada biza tsakanin Najeriya da Daular Larabawa, wacce ‘yan cirani da masu yawon bude ido daga Najeriya ke ribibin zuwa.

A watan Satumbar daya gabata, Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gana da Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa, Muhammad Bin Zayed Al-nahyan, a birnin Abu Dhabi, domin daidaita dangantaka tsakanin kasashen biyu.

A kwanakin baya, Ministan Sufurin Jiragen Saman Najeriya, Festus Keyamo, ya bayyana cewar kamfanin jiragen saman emirates ya bada takamaimiyar ranar dawowa harkokinsa a filayen jiragen saman Najeriya.

Saidai, har yanzu Hadaddiyar Daular Larabawan bata bayyana shawarar da yanke akan baiwa matafiyan Najeriya bizar shiga kasar a hukumance ba.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG