‘Yan Najeriya daga shiyoyin kasar kama daga Kano, Filato, Bauchi, Kaduna, Neja da dai sauransu sun ce lallai kungiyoyin sun rufe ofisoshin DisCos amma ba su ga wani tasiri da zanga-zangar ya yi a kasar ba.
Shugaban Hukumar bada agajin gaggawa na jihar Yobe wato YOSEMA, Dakta Mohammed Goje ne ya bayyana hakan a yayın hira ta musamman ga Muryar Amurka.
Wata majiyar soji ta bayyana cewar an samu nasarar kubutar da mutanen ne sakamakon samun wani kiran gaggawa a ranar 11 ga watan Mayun da muke ciki, da misalin karfe 12 rana.
Shigar da karar ya biyo bayan faifan bidiyon daya karade shafukan sada zumunda a ‘yan makonnin da suka gabata inda aka wasu dalibai suna cin zalin Namitra Bwala.
Matakin ma’aikatan na zuwa ne biyo bayan umarnin hadin gwiwa da kungiyar kwadago ta Nlc da takwararta ta Tuc suka baiwa mambobinsu a karshen mako na cewa su kargame ofisoshin domin nuna adawa da karin kudin wuta.
A ranar Alhamis wasu ‘yan bindiga suka kutsa jami’ar kimiyya da fasaha ta Confluence da ke Osara a jihar Kogi suka kwashi dalibai da dama suka yi cikin daji da su.
Shugaba Bola Tinubu ya bukaci Babban Bankin Najeriya da ya dakatar da aiwatar da dokar haraji ta yanar gizo da ya dora kan 'yan kasa wacce aka fi sani da cybersecurity levy, sannan ya bayar da umurnin a sake nazarin matakin.
Ododo ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyarar ganewa idonsa jami’ar ta Confluence University a ranar Asabar.
Kwana biyu bayan kaddamar da katin lamuni na kudin dala a Najeriya, wato American Express Credit Card, irinsa na farko a Afrika, masana tattalin arziki sun fayyace bambancinsa da kudin Crypto, yayin da masu masana’antu ke cewa, akwai bukatar wayar da kan ‘yan kasuwa akan alfanun aiki da katin.
A ranar 23 ga watan Afrilun daya gabata ne, kotun ta umarci Hukumar EFCC ta mikawa tsohon gwamnan takardar sammaci ta hannun lauyansa game da tuhume-tuhumen halasta kudaden haram da ake yi masa.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.