Karanci da tsadar man fetur na ci gaba da barazana ga harkokin yau da kullum a tsakanin ‘yan Najeriya, musamman a manyan biranen kasar. Kano na daga cikin wuraren da wannan matsala ke kawo cikas ga jama'a, inda ake sayar da lita daya ta mai daga naira dari tara da hamsin zuwa dubu daya.
A daidai lokacin da karanci da tsadar man fetur ke kara kamari a kusan dukkan sassan Najeriya, an sami sabani da ka iya tsananta matsalar tsakanin bangarorin da lamarin ya shafa, kamar kungiyar ciyamonin depot-depot na IPMAN, kamfanin NNPCL da ma hukumar NMDPRA.
Hakan ya biyo bayan wani kudiri mai matukar mahimmanci ga kasa da dan majalisar, Umar Ajilo, ya gabatar inda yake bayyana damuwa game cigaba da samun dogayen layuka a gidajen man dake fadin Najeriya.
A yayin zaman kotun, Tukur Mamu ta hannun lauyansa, Abdul Muhammad, yayi zargin cewar hukumar tsaro ta DSS ta sabawa umarnin da kotun ta bayar a ranar 19 ga watan Disambar 2023, na cewa a barshi ya rika ganin likitansa domin duba lafiyarsa.
Yayin hirarsa da manema labarai a birnin Damaturu, Kwamishinan Lafiya na yobe, Dr. Lawan Gana, ya musanta rahotannin dake yawo a kafafen sada zumunta game da zargin mutuwar mutane 200 a kananan hukumomin Potiskum da Nangere na jihar.
Dillalan mai a Najeriya sun dora alhakin karancin fetur na baya-bayan nan akan tsarin da babban kamfanin man fetur na kasar, NNPCL, ke bi wajen samar musu da shi.
Tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya ya bayyana cewar babu wata kotun jiha a Najeriya da zata iya sauraron shari’ar da ake yi masa kan zargin cin amanar mukami kasancewar hakan zai iya bijiro da batun dacewar hakan bisa tanade-tanaden kundin tsarin mulki dana shari’a.
‘Yan Najeriya na ci gaba da kokawa game da yadda karancin man fetur da kuma tsadarsa ta mamaye arewacin kasar, bisa yadda al’umma ke shan wahalar samun wannan makamashi da rayuwa ta dogara da shi. Yanzu haka farashinsa ya yi tashin gwauron zabi ya wuce farashin gwamnati.
A shekarar da ta gabata jim kadan bayan da aka rantsar da shi, Tinubu ya cire tallafin mai da gwamnati ke biya wanda ke saukaka farashin mai ga al’umar kasar .
Najeriya ta samu jarin dalar Amurka miliyan 600 na samar da kayayyakin aiki a tashar jiragen ruwa daga kamfanin jigilar kayayyaki na kasar Denmark A.P. Moller-Maersk MAERSKb.CO, kamar yadda fadar shugaban kasar ta fitar ranar Lahadi.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.