Lauyan Cubana Chief Priest ya shaidawa kotun cewar dukkanin bangarorin sun bukaci a sasanta takaddamar a bisa dacewa da tanade-tanaden sashe na 14(2) na dokar Hukumar EFCC.
A yau Alhamis, jami’an Rundunar ‘Yan Sandan Legas, suka kama wasu mutane 50 dangane da arangamar wasu bata-gari a shahararriyar kasuwar kayan abincin nan ta Ile-Epo dake karamar hukumar Alimosho ta jihar.
Kwamishin Muhalli da Albarkatun Ruwa na Legas, Tokunbo Wahab, ya bayyana cewar gwamnatin jihar ta gano gidaje 86 a karkashin gadar Dolphin Estate, dake yankin Ikoyi, inda ‘yan haya kan biya Naira dubu 250 a matsayin kudin haya.
Daraktan Yada Labarai na Ma’aikatar Tsaron Najeriya, Edward Buba, ne ya bayyana wa manema labarai hakan a yayin hirar da yayi dasu a shelkwatar tsaron kasar dake birnin Abuja, a yau Alhamis.
Gwamnan Jihar Ebonyi a Najeriya, Francis Nwifuru, ya sake bayar da karin Naira 10,000 ga albashin ma’aikatan jihar.
Yaran masu kananan shekaru ciki har da jinjira wadda bata wuce 'yan makonni ba da haihuwa, an sace su daga Sakkwato aka kai su babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, kafin dubun wadanda ake tuhuma ta cika.
Sakon sugaban na Najeriya yazo ne a wani sako da fadar gwamnatin Najeriya ta fitar a ranar Litinin 1 ga Mayu, na bikin ranar ma’aikata, ta hanun mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Cif Ajuri Ngelale.
Kwamitin kula da harkokin albarkatun man fetur na majalisar wakilan yayi kiran ga jami’an tsaro da su dira ma yan kasuwan da ke boye man fetur din suke kuma tsawwala farashin man yadda suka ga dama.
Ajero yace, "tsohon tsarin mafi karancin albashi na naira dubu 30 ya daina aiki tun a ranar 18 ga watan Afrilun daya gabata, kuma a yau kamata yayi a ce muna amfani da sabon tsari, ya kamata ce mun kammala tattaunawa akan hakan".
Ranar ma'aikata wani biki ne da akan yi duk ranar 1 ga watan Mayun kowace shekara domin karrama irin gudunmowar da ma'aikata kan bayarwa a fadin duniya da kuma muhimmiyar rawar da suke takawa wajen gina al'umma da tattalin arziki.
Ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar bayan taro da Shugaban Kungiyar Mamallaka Rumbunan Adana man, wanda wani reshe ne na IPMAN, Yahaya Alhassan ya fitar a Abuja game da gaza biyan hakkokin dillalan na tura man.
A ranar Talata ne Najeriya ta kara wa ma’aikatan gwamnati albashi da kashi 25% zuwa 35%, tun daga watan Janairu da ya gabata, in ji hukumar albashi, yayin da kasar mai mafi girman tattalin arziki a Afirka ke fama da matsalar tsadar rayuwa na kusan shekaru talatin.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.