Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Dakatar Da Sabon Tsarin Harajin Yanar Gizo


Ministan yada labarai, Mohammed Idris (Hoto: Facebook/Ministry of Information)
Ministan yada labarai, Mohammed Idris (Hoto: Facebook/Ministry of Information)

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta dakatar da harajin yanar gizo mai cike da cece-kuce a hada-hadar bankunan na'ura mai kwakwalwa.

WASHINGTON, D. C. - Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a na Najeriya Mohammed Idris ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar gwamnatin kasar bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) a fadar ta gwamnati da ke Abuja ranar Talata.

Ya ce ana kan kara yin nazari kan tsarin.

“Matsayin gwamnati shine an dakatar da wannan tsarin. An dage shi. Matsayin gwamnati kenan a yanzu. Ana kan sake nazarinsa. Abin da aka jaddada kenan a wani taron majalisar Ministoci (FEC) a jiya.

Kun san cewa majalisar ta yau (wato taron) ci gaba ne na zaman majalisar na jiya,” in ji Ministan. “Don haka, zan iya gaya muku cewa an dakatar da harajin yanar gizo. Gwamnati na kan nazarinsa.”

A ranar 6 ga watan Mayu ne Babban Bankin Najeriya (CBN) ya umarci bankuna, masu gudanar da hada-hadar kudi ta wayar salula, da masu bada kafar biyan kudi da su aiwatar da wannan harajin kamar yadda yake kunshe a cikin dokar haramta kutsen yanar gizo (Wato Hani, Kandagarki, da sauransu) (Gyara) ta 2024.

Da wannan, duk ma'amalar kafar lataroni ana tsammanin za su jawo harajin 0.5 bisa ɗari. Za a aika da kudin ne zuwa asusun ajiyar yanar gizo na kasa wanda ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA) ke kula da shi.

Sai dai an tari matakin da fushi matuka, lamarin da ya sa ake kiran da a dakatar da shi.

A makon da ya gabata ne Majalisar Wakilai ta bukaci CBN da ya janye daftarin da ya umarci cibiyoyin hada-hadar kudi da su fara aiwatar da harajin kashi 0.5 cikin 100 na yanar gizo, inda ta bayyana hakan a matsayin “mai cike da rudu”.

Wannan al’amarin ya kasance ne biyo wani kudiri kan bukatar gaggawa ta dakatarwa da kuma gyara tsarin aiwatar da harajin yanar gizo din da Kingsley Chinda ya gabatar.

A cewar Green House, bankin CBN zai janye umurnin farko, kuma ya "fitar da abin da za a fi fahimta".

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG