Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso ne ya bayyana daukan wannan matakin jim kadan bayan kamalla taron manufofin kudi na yini biyu a yau Talata inda aka kara kudin ruwa da maki 150 kuma a yanzu yake kan kaso 26 da digo 25.
Yayin da take gabatar da kudirin mai matukar mahimmanci ga kasa, majalisar ta bukaci Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo ya gudanar da cikakken bincike akan ma’aikatan dake aiki a tashoshin jiragen saman najeriya.
Kungiyoyi masu faftuka na nuna shakku tare da zargin rundunar 'yan sanda da yin rufa-rufa da batun jami'ar 'yar sanda da aka kama da hannu ga satar kananan yara daga Sakkwato har zuwa Abuja.
Hukumomin tsaro basu tabbatar da harin ba ko adadin wadanda suka rasa ransu da wadanda suka jikkata.
Majalisar Dokokin ta doshi cika shekara guda tun bayan da aka rantsar da mambobinta yayin da wannan wata na Mayu Gwamnatin Bola Tinubu ke shirin cika shekara guda da karbar mulki.
Dakarun runduna ta daya ta sojojin Najeriya da ke aiki a yankin Kaduna sun ce sun halaka 'yan ta'adda bakwai a kauyen Udawa da ke karamar hukumar Chikun a jihar.
Dakarun, karkashin jagorancin Burgediya Janar Diwa, sun yi nasarar kwato ababen hawa da makaman da a baya 'yan taaddar suka kwata daga hannun dakarun Najeriya a ganiyar rikicin Boko Haram.
Da yake zartar da hukunci akan batun a yau Litinin, Mai Shari'a Ekwo ya kafa hujja da yawaitar fasa gidajen yari a matsayin dalilin kin amincewa da bukatar mayar da shi gidan gyaran hali na Kuje.
Bayanai sun tabbatar cewa wannan daurin aure na 'yan mata 100 yana nan daram kamar yadda aka tsara a ranar 25 ga wannan watan na Mayu.
A daidai lokacin da rade-radin daina amfani da tsoffin takardun kudin Naira ya karade kafofin sada zumunta, Ministan yada labaran Najeriya Muhammad Idris, ya ce babu wannan magana.
A cewar NELFUND, dalibai zasu neman rance domin cimma burinsu na karatu ba tare da wata matsala ba.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.