Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin Kwadago Sun Yi Fatali Da Tayin Naira Dubu 48 A Matsayin Mafi Karancin Albashi


Kungiyar NLC
Kungiyar NLC

Shugaban Kungiyar Kwadago ta NLC, Joe Ajero, ya bayyana cewar ba da gaske gwamnatin tarayyar take ba a tattaunawarta da 'yan kwadagon game da sabon mafi karancin albashi.

Kungiyoyin Kwadago da suka hada da NLC da TUC sun fice daga tattaunawar da ake yi akan mafi karancin albashi a Najeriya data kunshi bangarorin gwamnati dana kamfanonin masu zaman kansu.

Sakamakon fusatar da suka yi da tayin Naira dubu 48 da gwamnatin tarayya tayi musu a matsayin mafi karancin albashi, yasa kungiyoyin kwadagon suka bayyana da shirme.

Shugaban Kungiyar Kwadago ta NLC, Joe Ajero, ya bayyana cewar ba da gaske gwamnatin tarayyar take ba a tattaunawarta da 'yan kwadagon game da sabon mafi karancin albashi.

Inda yace gwamnatin tarayyar ba ta da bayanan da suka dace domin tattaunawa da 'yan kwadagon.

Ajearo ya cigaba da cewar sun baiwa gwamnatin nan da karshen wata ta tsaida matsaya, inda yace kungiyar kwadago za ta tsaida ta ta matsayar bayan cikar wa'adin.

Kungiyar kwadago ta TUC ta samu wakilcin Mataimakin Shugabanta, Mr. Tommy Okon a tattaunawar.

An ruwaito wani bangare na sanarwar hadin gwiwar da Ajero da Okon suka rattaba wa hannu na cewar, "ba wai kawai dan tayin naira dubu 48 da gwamnatin tarayyar tayi a matsayin mafi karancin albashi ya kasance wasa da hankulan ma'aikatan Najeriya ba saidai yayi matukar gaza bukatu da burukanmu."

A baya, kungiyoyin kwadagon NLC da TUC sun yiwa gwamnatin tarayyar Najeriya tayin Naira dubu 615 a matsayin mafi karancin albashi, inda suka bada misali da tsadar rayuwa a matsayin ma'aunin auna wannan tayin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG