Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar ya ce akwai matakan da ya kamata a dauka kafin gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa ta koma baiwa ‘yan Najeriya takardar izinin shiga kasar.
Alkalin Alkalan Najeriya, Mai Shari’a Olukayode Ariwoola yayi sammacin Babban Joji a Babbar Kotun Tarayya, Justice John Tsoho da takwararsa ta Babbar Kotun Jihar Kano, Mai Shari’a Dije Aboki akan bada umarni masu cin karo da juna game da masarautar Kano, abinda ya haifar da rudani a jihar.
Nan bada jimawa ba Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai gabatar da karamin kasafin kudin bana ga Majalisar Dokokin Kasar.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ne ya tabbatar da hakan yayin zaman hadakar majalisar a yau Laraba.
Sai dai wasu 'yan majalisar sun nuna takaicinsu kan wannan mataki da majalisar ta dauka.
Malaman addini da wani ‘dan majalisar dokokin jiha sun dakatar da shirinsu na aurar da mata da ‘yan mata 100 a yankin Arewacin Najeriya bayan da lamarin ya haifar da bacin rai.
Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar, Abba Morro ne ya fara gabatar da kudirin neman a dawo da dakataccen sanatan a yau Talatar, inda ya bayyana nadama a madadinsa.
Kudirin, wanda cikin hanzari ya tsallake karatu na 1 dana 2 a Alhamis din data gabata, yanzu haka yana dakon sa hannun Shugaba Bola Tinubu domin zama doka.
A sanarwar daya fitar, Akawun Majalisar Tarayyar, Sani Tambuwal, yace Shugaban Kasar zai yiwa 'yan majalisun jawabi ne game da halin da kasa ke ciki tare da kaddamar da dakin karatun majalisar.
Hukumomin sun ce "sun zo ne a kan babura kusan 100 kowannensu dauke da mutane uku."
Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya yi kira ga kawayen kasar da a hada kai domin magance matsalar ‘yan gudun hijira a kasar.
Domin Kari
No media source currently available