A ranar 23 ga watan Afrilun daya gabata ne, kotun ta umarci Hukumar EFCC ta mikawa tsohon gwamnan takardar sammaci ta hannun lauyansa game da tuhume-tuhumen halasta kudaden haram da ake yi masa.
Kudirin dai ya samu amincewar rinjayen ‘yan Majalisar ta dattawa, kuma ya tsallake mataki na biyu.
Ziyarar ta Harry na kwana uku domin halartar bukukuwan cika shekara 10 da kadamar da wasannin 'Invictus Games' na sojojin da aka raunata a fagen daga.
Kungiyoyin fararren hula da masana shari’a a Najeeriya sun fara jan hankalin gwamnati cewa kada ta yarda a yi tsarin sasantawa a wajen kotu ko kuma "Plea Bargain" a turanc, wato ba da wani kason kudin da ake zargi don a rufe batun.
Hedkwatar tsaron Najeriya ta ce da sanyin safiyar Juma’a Yarima Harry zai gana da Babban Hafsan Hafsoshin rundunar tsaron Najeriya, Janaral Christopher Gwabin Musa.
Sanarwar da ta musanta zargin, wanda mai magana da yawun Ministan Yada Labarai, Rabi'u Ibrahim ya sa hannu, ta ce bita da kulli ne kawai, kuma kage kamfanin ya yi wa gwamnatin ko kuma jami'anta.
Gwamnatin jihar Kaduna ta fito da wani tsari na hada makarantu 359 wuri daya saboda karuwan ayyukan ‘yan fashin daji lamarin da yasa aka samu yawan sace mutane da yin garkuwa dasu a jihar.
An gurfanar da Hadi Sirika ne a gaban Mai Shari’a Sylvanus Oriji na babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin Abuja tare da diyarsa, Fatima, da surkinsa, Jalal Sule Hamma, da wani kamfani mai suna Al Buraq Global Investment Limited.
Hakan wani martani ne ga bukatar gaggawa da dan majalisa Kingsley Chinda ya gabatar yana bukatar a dakatar tare da yiwa shirin aiwatar dokar harajin tsaron intanet din kwaskwarima.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.