Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Emefiele Ya Musanta Zargin Buga Takardun Naira Miliyan 684.5 Da Naira Biliyan 18.96


Tsohon Shugaban Babban Bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele
Tsohon Shugaban Babban Bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele

Emefiele ya musanta zargin ne a yau Laraba yayin da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta gurfanar da shi a gaban mai shari’a Maryann Anenih na babbar kotun babban birnin tarayya Abuja, bisa tuhume-tuhume hudu.

Dangane da tuhumar da ake ma tsohon Gwamanan Babban Bankin Najeriya Na CBN, Godwin Emefiele na bayar da izinin buga Naira miliyan 684.5 kan kudi Naira biliyan 18.96, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya mai fama da badakaloli daban-daban kan yadda ya tafiyar da harkokin kudade na babban bankin na Najeriya a lokacin da yake shugaban CBN, ya musanta zargin

Emefiele ya musanta zargin ne a yau Laraba yayin da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta gurfanar da shi a gaban Mai Shari’a Maryann Anenih na babbar kotun babban birnin tarayya Abuja, bisa tuhume-tuhume hudu.

Hukumar EFCC ta zargi Emefiele da karya doka da nufin cutar da jama’a a lokacin da ya aiwatar da tsarin sauya kudade a zamanin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, kamar yadda tuhume-tuhume hudu da aka gabatar masa.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kuma zargi Emefiele da amincewa da cire Naira biliyan 124.8 ba bisa ka’ida ba daga asusun tara kudaden shiga na tarayya.

~Yusuf Aminu Yusuf~

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG