Dakarun, karkashin jagorancin Burgediya Janar Diwa, sun yi nasarar kwato ababen hawa da makaman da a baya 'yan taaddar suka kwata daga hannun dakarun Najeriya a ganiyar rikicin Boko Haram.
Da yake zartar da hukunci akan batun a yau Litinin, Mai Shari'a Ekwo ya kafa hujja da yawaitar fasa gidajen yari a matsayin dalilin kin amincewa da bukatar mayar da shi gidan gyaran hali na Kuje.
Bayanai sun tabbatar cewa wannan daurin aure na 'yan mata 100 yana nan daram kamar yadda aka tsara a ranar 25 ga wannan watan na Mayu.
A daidai lokacin da rade-radin daina amfani da tsoffin takardun kudin Naira ya karade kafofin sada zumunta, Ministan yada labaran Najeriya Muhammad Idris, ya ce babu wannan magana.
A cewar NELFUND, dalibai zasu neman rance domin cimma burinsu na karatu ba tare da wata matsala ba.
Ministar Mata, Uju Kennedy -Ohanenye, ta janye karar da ta shigar a kan kakakin majalisar dokokin jihar Niger, Abdulmalik Sarkindaji, akan aniyar sa ta auren marayu 100 daga mazabarsa.
A cewar Hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya ta’annati, an gurfanar da ‘yan Chinar ne a ranar Litinin 22 ga watan Afrilun daya gabata tare da kamfaninsu mai suna, Ebuy Concept Limited, akan tuhuma guda dake da nasaba da hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba.
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta hana bada belin Tigran Gambaryan, babban jami’in kamfanin hada-hadar Kudi ta Yanar gizo Binance.
Kafaffen yada labaran cikin kasar Najeriya sun ruwaito cewar Shugaban na Sengal ya zo ziyarar aiki a Najeriya ne.
Ana zargin wani matashi, Shafi'u Abubakar, wadda aka ruwaito cewar, ya bayyana wata dadaddiyar takaddamar rabon gado a matsayin dalilinsa na haddasa fashewar.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.