WASHINGTON DC - Majalisar Bunkasa Tattalin Arzikin Najeriya ta (NEC) ce ta bayyana hakan a jiya Alhamis a rahoton da aka gabatar mata yayin taronta na 140 wanda ya gudana ta allon gani a karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima.
Ministan Kasafi da Tsare-Tsaren Tattalin Arziki, Atiku Bagudu wanda ya yiwa manema labaran fadar gwamnati jawabi ta na'ura yace daga cikin gwamnonin Najeriya 36, har yanzu gwamnonin jihohi 20 da birnin tarayya, Abuja, basu bayyana matsayarsu ba.
Saidai bai fayyace sunayen jihohin ba
Gwamnonin da suka gabatar da matsayarsu a rubuce sun kuma bukaci a yiwa kundin tsarin mulkin kasa garanbawul.
A wani labarin kuma, Majalisar Tattalin Arzikin ta kuma karbi takaitaccen rahoton wucin gadi akan matsalar satar danyen mai da hanyoyin maganceta
Kwamitin ya fayyace wuraren da ake samun zurarewa a bangaren albarkatun man fetur a yayin daya tantance wuraren da ake yawan samun karya doka.
Kwamitin, karkashin jagorancin Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya bukaci samun kudirin gwamnati wajen aiwatar da sauye-sauye.
Dandalin Mu Tattauna