Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Caccaki Kungiyar NLC Game Da Zanga-zangar Da Ta Yi


Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah wadai da zanga-zangar da kungiyar Najeriya NLC ta yi  a fadin kasar domin nuna adawa da tsadar rayuwa da yunwa, inda ya gargadi kungiyar kwadago da ta sani cewa, ba ita kadai ce muryar jama’a ba.

Shugaba Tinubu, ya yi magana ne a yayin kaddamar da layin dogo na zamani a Legas wanda ya hada daga Agbado zuwa Oyingbo a jiya Alhamis.

A ranar Talata ne kungiyar kwadago ta gudanar da zanga-zangar nuna adawa da tsadar rayuwar da ake ciki da rashin aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma wa.

Zanga-zangar tsadar rayuwa da NLC ta gudanar
Zanga-zangar tsadar rayuwa da NLC ta gudanar

Tinubu ya ja kunnen NLC a yayin jawabinsa, inda ya ce ya kamata ta fahimci cewa, duk da ‘yancin da take da shi, ba za ta iya yakar gwamnatin da ba ta wuce wata 9 ba.

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa babu gudu babu ja da baya dangane da sauye-sauyen da ya faro duk da turjiyar da yake fuskanta daga wadanda ya kira ‘yan fasa-kwauri.

"Ku bar ni in gudanar da aiki na, ya kamata 'yan kwadago su fahimci cewa ba su kadai ke da yanci da hakki ba. Idan kuna son shiga zabe ne mu hadu a 2027. Idan ba haka ba, ku mana shiru a zauna lafiya, ba ku kadai bane kuke magana da muryar yan Najeriya." Inji Tinubu.

Ya kuma nanata cewa, yaki da cin hanci da rashawa na fuskantar turjiya, inda ya sha alwashin cewa, gwamnati za ta kawar da cin hanci da rashawa.

Tinubu ya ce wahalhalun da ake fuskanta a halin yanzu na cire tallafin man fetur da kuma hadewar farashin canji na wucin gadi ne, inda ya roki ‘yan Najeriya da su kara hakuri.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG