Tashin farashin dala kan naira na daga cikin manyan dalilan kunci a tsakanin talakawan Najeriya, inda hakan ya kara ta’azzara bayan janye tallafin fetur.
Har yanzu mizanin tsallake talauci na majalisar dinkin duniya na samun dala daya a wuni bai canja ba; amma dala daya ba za ta iya kosar da mutum daya ba.
Shugabannin kasuwar canji da jami'an yaki da cin hanci, EFCC, ke zargi da haddasa tashin farashin dala sun nuna farin ciki da toshe kafar sadarwar yanar gizo ta BINANCE da ke jagorantar saye da sayar da kudin ketare.
Abubakar Abdullahi Dauran, shugaban kasuwar canji ta Abuja, ya ce "BINANCE da 'yan Crypto ke tada farashin kudin, amma mu ko nawa dala ta kama mu na bin 'yar riba ce kadan kuma mu ma tsadar farashin kaya ya shafe mu don kasuwa daya mu ke ci da jama'a. "
Gwamnatin Najeriya ta ce ta na bin matakan samar da wadatacciyar dala ta hanyar masu zuba jari na ketare.
Muhammad Idris, ministan labaru na Najeriya, ya ce, "Ana maganar dala - dala to za mu jawo masu zuba jari daga ketare don wadatar da dalar a kasa kuma shugaba Tinubu ya samu nasarar yarjejeniyar shigo da jarin kimanin dala biliyan 30 da hakan zai taimaka wajen samar da ayyukan yi."
Masanin tattalin arziki a Abuja Yushau Aliyu ya ce face an koma aiki da Naira a cikin gida wajen hada-hadar kasuwanci da dillalan ketare ne da rage dogaro da shigo da kaya daga ketaren za a iya cimma muradin dawo da darajar Naira.
Kamar yanda wadanda a ke zargi da zama 'yan barandan tada farashin dala ta yanar gizo, haka ma wasu 'yan kasa ke yada bayanan saukar dalar da zummar hakan ya yi tasiri kan farashin da ba shi da tabbas.
Saurari rahoton Nasiru Elhikaya:
Dandalin Mu Tattauna