Jim kadan bayan da wasikar tsohon Shugaban Najeriya, kuma daya daga cikin wadanda suka kafa kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin nahiyar Afrika wato ECOWAS, Janar Yakubu Gowon mai ritaya, ya karade ko’ina a kafaffen yada labarai, masana a fannin tsaro, diflomasiyyar kasa da kasa, masu fashin bakin siyasa suka yi ta bayyana mabanbantan ra’ayoyi a kan tasirin wasikar ko akasin haka.
A hirar shi da Muryar Amurka, mai sharhi a kan siyasa da diflomasiyyar kasa da kasa kuma Shugaban kamfanin kasuwanci da zuba jari GITC, Mal. Baba Yusuf, ya ce wasikar ta zo a makare saboda irin tsauraran matakan da kungiyar ta dauka tun farko.
A wani bangare kuma, kwararre a fannin tsaro da diflomasiyar kasa da kasa, Kabir Adamu ya bayyana cewa, jadada mahimmancin rayuwa da walwalar dan adam da tsohon Shugaban ya yi a cikin wasikar sa zai iya taimaka wa sakon sa ya yi tasiri wajen dinke baraka tsakanin Shugabannin kungiyar ta ECOWAS .
A nata bayanin, wata matashiya ‘yar Jamhuriyyar Nijar tace al’umar kasarta na maraba da sakon na tsohon Shugaban Najeriya, tana mai cewa babu fatan da ‘yan Nijar ke da shi a halin yanzu kamar a bude musu iyakokin kasashen dake makwabtaka da su gabanin tunkarowar watan Ramadan.
Tun bayan kafa kungiyar ECOWAS a matsayin babbar hukumar shiyya ta yammacin nahiyar Afirka a shekarar 1975, ficewar mambobi uku lokaci guda shi ne mafi girman kalubalen da ta fuskanta a ‘yan shekarun baya-bayan nan.
Saurari cikakken rahoton:
Dandalin Mu Tattauna