Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Kamata 'Yan Najeriya Su Ba Gwamnatin Tinubu Lokaci -Gowon


Gowon da Tinubu
Gowon da Tinubu

Tsohon Shugaban kasar Najeriya, Janar Yakubu Gowon ya shawarci 'yan Najeriya cewa, kada yi saurin yanke hukunci kan ayyukan shugaba Bola Tinubu danganed a halin da kasar ke ciki.

Tsohon Shugaban kasar, ya yi wannan kiran ne a hirar shi da manema labarai, bayan ganawarsa da Shugaba Bola Tinubu a fadar Shugaban kasa da ke Abuja a ranar Laraba,

“Na fada masa cewa babu wani Shugaban da zai kai wannan matsayin da ba ba zai ji ko kuma ganin irin wadannan maganganun da korafe-korafen a da kanshi ba a kafafen sadarwa. Amma babu shakka daga abin da mutum yake ji da abin da yake gani a kafafen yada labarai daban-daban. Ina ganin gwamnati na iya bakin kokarinta wajen ganin ta shawo kan matsalolin da ke addabar kasar."

Ya kuma ce kowane Shugaban Najeriya dole ne zai ji irin wadanan suka, don haka ya bukaci Tinubu da kada ya damu da sukar da yake sha.

Tsohon Shugaban Najeriya Yakubu Gowon
Tsohon Shugaban Najeriya Yakubu Gowon

Sai dai ya roki ‘yan Najeriya da su baiwa Shugaban kasar dama domin a ganinsa, yana iya kokarin sa.

Da aka tambaye shi ra’ayinsa game da wahalhalun da ake fama da su a kasar, sai ya ce:

"A gani na, abun dai da mutum zai iya cewa shi ne 'yan Najeriya, dole ne mu bai wa Shugaban kasa lokaci domin ya yi abubuwa yanda su ka kamata. Kuma ka da a yi saurin sa ran ganin cikakken sakamako cikin hanzari. Wannan shine ra'ayina.”

Gowon ya ce ganawar da Shugaban kasar ta ta’allaka ne kan batun kalubalen da ke addabar yankunan ECOWAS, inda ya ce dole ne a sasanta.

“A matsayina na Shugaba da ke raye, ko kuma uban kungiyar ECOWAS, ina ganin sai mun tattauna a kan wasu tsare-tsare domin ganin abin da za a iya yi don shawo kan lamarin,”

Ya karyata ikirarin da aka yi a kafafen sada zumunta na yanar gizo cewa ya ki halartar taron da kungiyar ECOWAS ta shirya, inda ya kara da cewa, watakila hakan ya faru ne saboda rashin sadarwa.

“Ina ganin idan akwai wata rashin fahimta sai Shugaban kasa ya kira ni domin mu tattauna abin da zan yi.”

Da ya ke magana akan manufar ziyarsa fadar shugaban kasar, Janar Gowon ya bayyana cewa: “Wannan ita ce ziyara ta farko ga Shugaban kasar tun bayan rantsar da shi, ko da ya ke na je bukin rantsar da shi domin in yi masa fatar alheri da kuma yi mashi fatar samun nasara."

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG