Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bada Damar Jefa Kuri’ar Raba Gardama Zai Taimaka Wajen Warware Batun Kafa Masarautun Jihar Kano - Masana


Kungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya ta kaddamar da kwamitin hada sarakuna a cikin tsarin mulkin kasar
Kungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya ta kaddamar da kwamitin hada sarakuna a cikin tsarin mulkin kasar

Majalisar dokokin Kano ta yi karin haske dangane da mabanbantan wasikun da take karba daga kungiyoyi masu neman a sake fasalin dokar data kafa masarautun jihar guda biyar, sai dai masana na cewa, bada damar jefa kuri’ar raba gardama zai taimaka wajen waware wannan batu cikin ruwan sanyi.

Wata kungiya mai maradun dawo da sarkin Kano Sanusi na biyu ce ta fara mika wasika zauren Majalisar kimanin makonni uku da suka gabata ta neman Majalisar ta rushe masarautu hudu da gwamnatin Kano ta Abdullahi Umar Ganduje ya kirkiro kusan shekaru biyar da suka shude.

Daga bisani aka rinka samun kwararar wasiku daga sassan sabbin masarautun suna jaddada goyon bayan su ga ci gaba da wanzuwar masarautun tare da jan hankalin ‘yan Majalisar dokokin ta Kano kan hadarin dake tattare da rusa masarautun da kuma dawo da Sanusi karagar Mulki.

Ko da yake Majalisar dokokin ta Kano bata kai ga fara mahawara ko tattaunawa ba akan wannan batu ba, Shugaban masu rinjaye na Majalisar Hon Lawan Hussaini ya yi karin haske dangane da halin da ake ciki inda ya bayyana cewa, “Idan policy wato manufar gwamnati ya yi dai dai da abin da mutane suke kawo mana to za mu gaggauta aiki da irin bukatu ko sha’awarta, mu muna saurarorin sha’awar gwamnatin mu ta karkashin jam’iyyar mu ta NNPP ne”.

To amma masana dake sharhi kan lamuran Jama’a, sun fara tsokaci tare da bada shawarwari ga gwamnati da Majalisar dokokin ta Kano game da hanyoyin da su ka kamata su bi wajen warware wannan takaddama cikin lumana.

A hirar shi da Muryar Amurka, Dr Sa’idu Ahmad Dukawa, masanin kimiyyar siyasa da harkokin Mulki dake koyar da wannan fanni a Jami’ar Bayero, Kano na cewa, “Kamata ya yi su gudanar da kuri’ar raba gardama ko ra’ayin Jama’a, sahihiya, wadda a turanci ake kira “referendum”, wadda a tsarin musulinci akwai ta, a tsarin demokaradiyya akwai ta kuma hakan ita ce hanya sahihiya da za’a kaucewa, fuskantar barazanar tsaro game da lamarin”.

Yayin da wasu mutane ke amfani da kungiyoyi wajen matsawa gwamnati da Majalisar dokoki lamba kan bukatar ci gaba da wanzuwar masarautu biyar a jihar Kano ko kuma a rusa 4 a bar daya, babban burin galibin al’ummar jihar shine gwamnati ta magance halin matsin rayuwa da ‘yan Najeriya ke ciki.

Saurari cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG