Shugaban Amurka Donald Trump yace akwai yiyuwar ganawa da Vladimir Putin “nan bada jimawa ba”, inda yace yana da yakinin cewar da gaske takwaran nasa na Rasha na nufin kawo karshen yakin Ukraine.
Babu wani bayani a game da murnar zagayowar maulidin haihuwar shi a Mount Vernon cikin bayanan da aka adana, yayin da kundin rubutun shi ya yi nuni da cewa shi haziki ne a faggen aiki.
Mataimakin shugaban kasar Amurka JD Vance ya yi kashedi ga kawayensu na Turai da suke halaratan taro kan tsaro a Munich na kasar Jamaus game da barazanar cikin gida.
Dan Majalisar Dokokin Amurka, Scott Perry, ya bayyana cewa hukumar raya kasashe ta Amurka (USAID) ke samar da kudade ga kungiyoyin ‘yan ta’adda, ciki harda boko haram.
Ga dukkan alamu takaddamar cinakayya a matakin kasa da kasa sai ma abin da ya yi gaba, saboda Trump ya ce babu gudu ba ja da baya.
Yayin da Shugaba Trump ke ta lafta haraji kan kayakin kasashen waje, a gefe guda kuma ya bukaci a rage kudin ruwa a cikin gida don saukaka hada hada.
Trump ya nanata ikirarin da yayi a lokacin yakin neman zabensa na 2024 cewar FEMA ta kashe miliyoyin daloli cikin rashin adalci a martaninta ga mummunar guguwar da ta afkawa jihar North Carolina a watan Satumban da ya gabata, inda ta hallaka fiye da mutane 100.
Sallamar Paul Martin na zuwa ne kwana guda bayan da ofishinsa ya fitar da wani rahoto da ya caccaki yadda gwamnatin Trump ke kokarin wargaza hukumar.
Dusar kankarar mafi yawa da ake hasashe ta sauka zata kai centimita 25, wanda ake hasashen zai kasance a wani yankin arewaci da tsakiyar jihar Virginia da gabashin yammacin Virginia
Yana zargin cewa tsauraran matakan kauce ma bayar da cin hanci da rashawa ga jami'an kasashen waje da aka gindaya ma Amurkawa, na hana kasuwancin Amurka gogayya a kasuwannin duniya.
Shugaban na Amurka ya nuna alamar cewa ba zai sauya matsaya ba game da shirin Amurka na karbe iko da Gaza tare da debe firgitattun mazauna cikinta da kuma sauya yankin da yaki ya daidaita.
Domin Kari
No media source currently available